Batun yara miliyan biyar masu fama da yunwa a Nijeriya

Spread the love

Ƙungiyar Agaji ta Likitoci – Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ce a cikin watanni takwas ɗin farko na wanan shekarar 2024 ta bayar da magani ga ƙananan yara 52,725 masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a arewacin Nijeriya. 

Shugaban MSF, Dr Christos Christou, ya shaida wa manema labarai a Abuja a ƙarshen mako cewa adadin yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jikin ya ninka a arewacin Nijeriya. 

Ya ce daga watan Janairu zuwa Agusta, MSF ta tattara alƙaluma da ke cewa an samu ƙarin ƙananan yara da ake kwantarwa asibiti saboda da kashi 51 cikin 100.

”Ana cikin haka kuma sauran cutuka masu kama ƙananan yara sun samu damar shiga jikin yara da dama a Nijeriya,” inji shi. 

Dr Christou ya ƙara da cewa sun yi maganin sauran cutuka ga ƙananan yara 12,500 bayan waɗanda ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, lamarin da ke nuna cewa yawansu ya ruɓanya wanda aka samu a bara.

Mummunar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta yi ƙamari a jihohi shida na Arewacin Nijeriya, wani lamari mai matuƙar tayar da hankali, inda matsalar ta shafi yara ‘yan ƙasa da shekara biyar miliyan biyar da mata masu juna biyu kusan 600,000, a cewar Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP).

Matsalar na ci gaba da yaɗuwa cikin sauri.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar ɗinkin Duniya ya ce adadin yaran da ke fama da matsalar ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da bara.

Daraktar kula da harkokin lafiya a ƙungiyar Likitoci masu Bayar da Agaji ta MSF, Catherine ɓan Oɓerloop ta ce a wasu wuraren a arewacin Nijeriya, adadin ya ninka kusan sau biyu.

“Akwai yiwuwar yaran za su fuskanci matsalolin da suka shafi girmansu da fahimtarsu yayin da suke tasowa,” inji ta, a lokacin da take faɗin irin illolin da za su iya shafar yaran.

“Za su iya fuskantar cikas wajen girma, akwai kuma yiwuwar cewa ƙwaƙwalwarsu ba za ta ginu yadda ya kamata ba; hakan zai haifar masu da matsaloli wajen neman ilimi. Kuma waɗannan yara su ne makomar Nijeriya.”

Nijeriya na fuskantar matsalar ƙarancin abinci a duk faɗin ƙasar. A tsakanin watan Janairu zuwa Afrailun 2024 an tabbatar cewa mutum miliyan 25 ba sa samun isashen abinci. Wannan adadin ya haura zuwa miliyan 32 a tsakanin watannin Yuni zuwa Octoban 2024, kamar yadda alƙaluman WFP suka nuna.

Amma matsalar ta fi ƙamari a Arewacin Nijeriya. Matsalar tsaro da tashe-tashen hankula na daga cikin manyan abubuwan da suka fi ta’azzara matsalar yunwa a yankin.

Yankin arewa maso gabashin ƙasar ya kasance cibiyar rikice-rikicen ƙungiyar Boko Haram tsawon sama da shekara 10, waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar ISIS. Boko Haram ta yi sanadin kashewa da kuma sace dubban mutane, ta kuma tilasta wa miliyoyi barin gidajensu domin neman mafaka a wasu yankunan Nijeriya, da kuma makwaftanta, Nijar, Chadi da Kamaru.

Yayin da jami’an tsaron Nijeriya suka mayar da hankali kan Boko Haram, rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da aka shafe shekaru ana fama da su, sun ƙara janyo rashin zaman lafiya a yankin.

A cikin shekaru takwas da suka wuce, ƙungiyoyin ’yan ta’adda da aka fi kira da ’yan fashin daji na satar mutane don neman kuɗin fansa, tare da kashewa da kuma yi wa wasu fyaɗe. Wannan ta’addancin ya tilasta wa dubban mutane – musamman namoma da makiyaya barin gonakinsu.

Sauyin yanayi ya ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin abinci yayin da yanayin zafi ke lalata amfanin gona.

A wannan shekarar, lokacin da ake fama da ƙarancin abinci ya zo da wuri kuma manoma sun ce yanayin bana shi ne mafi muni da suka gani a cikin shekara bakwai.

Nijeriya na kuma fuskantar hauhawar farashi, wanda ke ƙara janyo tsadar farashin kayan masarufi kamar abinci da man fetur, lamarin da ke janyo tsadar rayuwa mai tsanani.

Matsalar tsaro da ƙarancin isashen abincin da ake fuskanta a Arewacin Nijeriya za ta iya yin illa ga ƙasashen da ke makwaftaka da ita a Yammacin Afrika, a cewar masana.

“Matsalar za ta iya janyo a fuskanci ƙarancin abinci a sauran ƙasashen da ke Yammacin Afrika, wanda hakan zai janyo ƙarin mutanen da za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, da ƙaruwar ‘yan gudun hijira da kuma yiwuwar ƙara taɓarɓarewar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin, a cewar babban mai yin sharhi a ɓangaren da ke lura da tsattsauran ra’ayi na Cibiyar Tony Blair, Bulama Bukarti.

“Hakan zai tilasta wa ƙungiyoyin bayar da agaji karkata ‘yan kuɗaɗen da suke kashewa zuwa kan matsalar, lamarin da zai iya yin illa ga agajin da suke bayarwa kan wasu matsalolin, kamar rikice-rikice da ɓangaren lafiya, wanda hakan zai shafi zaman lafiya na yankin,“ inji shi.

ƙungiyoyin bayar da agaji kamar Medecins Sans Frontieres (MSF) sun yi gargaɗin cewa babu kuɗaɗen da ake buƙata domin magance wannan gagarumar matsalar.

“Mun sha nanata wa Majalisar ɗinkin Duniya da sauran masu tallafawa kan yadda matsalar harkar jin ƙai ke ƙara taɓarɓarewa a Arewa maso Yammacin ƙasar,” a cewar Ahmed Bilal, shugaban shirin na MSF a yankin.

A bisa tilas, Asusun Kula da Yara na Majalisar ɗinkin Duniya, UNICEF ya rage yawan tallafin da yake bayarwa daga ƙananan hukumomi 23 zuwa ƙananan hukumomi 14 a jihar Katsina, duk da dai asusun na ci gaba da ƙoƙarin ganin ya samo wasu ƙarin kuɗaɗen.

By ukarofi