Mataimakiyar shugabar ƙasar Amurka Kamala Harris ta fitar da wata takarda ɗauke da bayanan likitanta dangane da lafiyarta a ranar Asaba. Takardar da ta bayyana cewa tana cikin “kyakkyawan ƙoshin lafiya” kuma “tana da ƙarfin juriya ta jiki da ta ƙwaƙwalwa” da ake buƙata don yin aiki a matsayin shugaban ƙasa.
Harris ta bayyana bayanan lafiyarta a bainar jama’a don nuna bambancin ta da ɗan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump, wanda ya fitar da taƙaitaccen bayani game da lafiyarsa tsawon shekaru, ciki har da harsashim da ya bi ta kunnen sa ya kife a wanin yunƙurin kisa da aka kai masa.
Dokta Joshua Simmons, wani Kanar Sojan Amurka kuma likita ga mataimakiyar shugaban ƙasa, ya rubuta cewa Harris, mai shekaru 59, tana kula da lafiyarta matuƙa, tate da salon rayuwarta, kuma rahoton binciken watan Afrilun da ya gabata ya bayyana matuƙar cigaba ta fuskar lafiya.
Rahoton ya zo makonni uku kafin zaɓen Amurka da ake sa ran yi. Kuma ya nuna cewa, Harris “na da ƙoshin lafiyar jiki da kuma na ƙwaƙwalwa da ake buƙata don samun nasarar aiwatar da ayyukan fadar shugaban ƙasa, da zama kwamandan rundunar sojin ƙasa, da mulkin ƙasa bakiɗaya.”
Trump, mai shekaru 78, ya yi shakku kan lafiyar Shugaba Joe Biden lokacin da shugaban mai shekaru 81 ya nemi a sake zaɓe.
Tun lokacin da aka maye gurbin Biden akan tikitin da Harris, wanda ke da shekaru 59, kallo ya koma kan lafiyar Trump.
A watan Nuwamban da ya gabata, Trump ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar Biden ta hanyar fitar da wata wasiƙa daga likitansa wanda ya ba da rahoton cewa tsohon shugaban yana cikin “ƙoshin lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa.”
