Shirin kawar da talauci a duniya nan da 2030 ba mai yiyuwa ba ne -Bankin Duniya

Spread the love

Bankin Duniya ya bayyana cewar shirin sa na kawar da tsananin talauci a duniya nan da shekarar 2030 ba mai yiwuwa ba ne, saboda haka sai an samu ƙarin tsakanin shekaru 30 zuwa sama da haka kafin a cimma shirin.

Babban jami’in Bankin duniyar Aɗel ɓan Trotsenburg ya bayyana cewar yunƙurin rage talauci a duniya ya kusan tsayawa cik, ya yin da shirin su na shekarar 2020 zuwa 2030 ya zama mai wahala saboda matsalolin da aka fuskanta a baya cikin su harda annobar Korona da sauyin yanayi.

Jami’in ya ce kusan mutane miliyan 700 ne a duniya, ko kuma kashi 8 da rabi ke rayuwa a kan ƙasa da dala biyu da centi 15 kowacce rana, abinda ke nuna tsananin talaucin da suke ciki.

Bankin ya ce ko da nan da shekarar 2030 adadin ba zai gaza ƙasa da kashi 7 da rabi ba, lura da yadda matsalar ta fi ƙamari a yankin ƙasashen da ke kudu da sahara.

Alƙaluman bakin sun kuma bayyana cewar adadin mutanen da ke rayuwa ƙasa da dala kusan 7 ya kai kashi 44, kuma su ne ake kallo a matsayin waɗanda suka tsallake shingen talauci.

Bakin ya ce adadin mutanen da ke fama da talaucin bai yi wani sauyawa na azo a gani ba tun daga shekarar 1990 saboda ƙaruwar jama’ar da ake samu a duniya.

By ukarofi