Shugaba Tinubu ya sauya sunan ɗakin al’adu na ƙasa zuwa zuwa Farfesa Wole soyinka. Shugaban yayi wannan sanarwa ne yayin saƙon taya murnar gwarzon bikin cika shekera 90.
A wani sanarwa da Ajuri Ngelale ya sa wa hannu, ya ce ” a yau na taya duniya da samun mutum mai zaburar da matasa. Da irin rawar da ya taka wajen yaƙar mulkin soja.
Ya kara da cewa,hanyar su ta haɗu wajen gwagwarmaya neman dimukraɗiya.
Sai daga ƙarshe shugaban ya taya gwarzon murna cika shekaru 90, tare da lafiya mai ɗorewa
