Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a jiya Alhamis ya gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, NLC da kuma TUC kan batun sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
To sai dai kuma tattaunawar ba ta kammalu ba, inda za a ci gaba da tattaunawa cikin sati mai zuwa kamar yadda rahotanni suka nuna.
Zaman ganawar da Shugaba Tinubu ya kira, ya gudana ne a Ofishin Shugaban Ƙasa da ke fadar gwamnatin tarayya Abuja.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron da ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu ana yi, ƙaramin minista a ma’aikatar ƙwadago da samar da ayyukan yi, Hon Nkeiruka Onyejeocha, ya bayyana taron a matsayin tattaunawa tsakanin yara da iyaye da yara.
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa taron tattaunawa ne na ganin yadda za a kyautatawa ma’aikata, inda ya ƙara da cewa ba a yi magana takamammen alƙaluma a tattaunawar da Shugaba Tinubu ya da mu ba, amma kuma mun yarda mu duba ainihin sharuɗɗan kuma mu sake haɗuwa cikin mako guda mai zuwa.
“To a nan ne muke. Domin ba mu je can muna magana Naira da Kobo ba. Aƙalla akwai wasu batutuwan da muka amince da su,” inji shi.
Ajaero ya kuma bayyana cewa, halin da ake ciki yana nan kamar yadda ya bayyana cewa NLC ta nace a kan Naira 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Nijeriya saɓanin N62,000 da gwamnatin tarayya ta tura.
A wani cigaban dai, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da wasu gwamnoni a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja jiya Alhamis.
An fara taron ne jim kaɗan bayan da shugaba Tinubu ya kammala tattaunawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon, waɗanda suka zo tattauna batun sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da AbdulRahman AbdulRazaƙ na Kwara, Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF); Charles Soludo na Anambra; da Usman Ododo na Kogi.
Yayin da ba a bayyana maƙasudin tattaunawar ba, ganawar ta biyo bayan wani gagarumin hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kan ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi a Nijeriya daga hannun gwamnoni.
Kotun Ƙolin ta ce, dole ne Gwamnatin Tarayya ta biya kai tsaye duk wani kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi ga waɗanda aka zaɓa a dimokraɗiyyance.
Kotun ta dakatar da gwamnonin daga yin katsalandan a al’amuran ƙananan hukumomi da aka zaɓa ta hanyar dimukraɗiyya, ta kuma umurci Gwamnatin Tarayya da ta hana wa ƙananan hukumomin da ba a zaɓa ba waɗanda gwamnoni ke naɗawa kuɗaɗensu.
Wannan hukunci da ya biyo bayan aarar da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ya shigar na neman samun cikakken ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi, ana ganin wata gagarumar nasara ce ga ƙananan hukumomi da Gwamnatin Tarayya bakiɗaya.
