
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da jagororin sojoji da sufeton ƴan sanda a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Waɗanda suka halarci zaman sun haďa da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa; Shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Shugaban Sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Kayode Egbetokun, sufeton ƴan sanda.

Ana ganin zaman ba zai rasa nasaba da sake farfaďowar ayyukan ta’addanci a wasu sassan Nijeriya musamman a shiyyar Arewa.
An gudanar da zaman ne gabannin ziyarar Shugaba Tinubu zuwa taron kaddamar da sabon Fafaroma, Pope Leo na XIV a Rome, biyo bayan gayyatar da Fadar Vaticanta yi masa.
Kakakinsa, Bayo Onanuga a wata takarda ranar Alhamis, ya ce Shugaba Tinubu zai haďu da manyan kasashen duniya ne a yayin kaddamar da Fafaroman, wanda shi ne Babban Bishop na Rome na 267 kuma jagoran Cocin Roman Katolika.
