Daga USMAN KAROFI a Abuja
Kansilan lafiya na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Haruna A. Ciroma, ya bayyana shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Anas Mukthtar Bello Danmaliki, a matsayin zakaran gwajin dafi daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, sakamakon jajircewa da kishin al’ummar yankin a cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannun Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.
Ya yi wannan yabo ne yayin da tawagar jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano ta kai ziyara babban asibitin Dawakin Tofa domin tantance buƙatun gyare-gyare da faɗaɗa ginin. A cewar Ciroma, ƙaramar hukumar ta buƙaci gwamnatin jiha ta samar da sabon ɓangaren taimakon gaggawa da kuma fadada ɗakin gwajin jini domin inganta aikin asibitin.
Wani daga cikin shugabannin tawagar, Architect Nazir Sa’id Ibrahim daga sashen tsare-tsare na ma’aikatar lafiya, ya ce tawagarsu ta samu umarni kai tsaye daga Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf domin gano muhimman buƙatun asibitin. Shugaban asibitin, Dakta Hussain, ya yaba wa gwamnatin Kano bisa ayyukan alheri da take aiwatarwa, tare da gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa jajircewa da ɗaukar sababbin ma’aikata don ƙara inganta harkar lafiya a yankin.
A nasa jawabin, Alhaji Anas Mukthtar Bello Danmaliki ya tabbatar da cewa za a aiwatar da dukkan gyare-gyaren da suka dace bisa sahalewar gwamnatin jiha, tare da cika alƙawarin ɗaukar sababbin ma’aikatan lafiya a Dawakin Tofa, domin tabbatar da ingantacciyar hidima ga al’umma.

