Shugaban ƙaramar Hukumar Funakaye ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Inuwa

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar Hukumar Funakaye, Honarabul Shuaibu Abdulrahman Adam, ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan ci gaba da kuma shugabanci mai hada kan al’umma a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja kuma aka rabawa manema labarai, shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a fannoni da dama da suka haɗa da bunƙasa jarin ɗan Adam, noma da kiwo, noman rani (irrigation), ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma gina ababen more rayuwa.

Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarƙirar ƙananan hukumomin cigaba (Deɓelopment Area Councils) guda 13, baya ga kananan hukumomi 11 da ake da su a jihar, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen inganta gudanar da mulki a matakin ƙasa.

Hon. Shuaibu Abdulrahman Adam ya yabawa gwamnatin jihar kan gyaran da kuma gina sabbin sakatariyoyin gwamnati na zamani, samar da fitilun tituna masu amfani da hasken rana, ciki har da na yankin Funakaye, da kuma faɗaɗa titunan cikin gari da na tsakanin al’umma a yankuna irin su Sangaru, Jalungo, Wakkaltu, Magaba, Feshingo da Bajoga.

Ya ce wadannan ayyuka sun taimaka matuka wajen inganta ayyukan gwamnati da kuma saukaka rayuwar al’umma a karkara.

Haka kuma ya yaba da gina kasuwanni da shaguna na zamani a Bajoga, da kuma gina gidan baki (guest house) a Funakaye tare da samar da ingantattun ofisoshi ga ma’aikata, da kuma dakunan taro masu dauke da hasken rana.

A ɓangaren tsaro, shugaban ƙaramar hukumar ya jinjina wa gwamnan kan matakan da ya dauka na inganta tsaro, ciki har da gina ofisoshin ‘yan sanda, kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro tsakanin Funakaye, Nafada da Kwami, da kuma tallafa wa jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai.

Ya buƙaci al’umma da su ci gaba da zaman lafiya da hadin kai domin dakile matsalolin tsaro.

A fannin lafiya kuwa, ya yabawa gwamnati kan horar da ma’aikatan lafiya, gyaran cibiyoyin kiwon lafiya da gina asibiti na zamani a Funakaye, tare da daukar sabbin ma’aikata har 28, da kuma samar da babura ga jami’an lafiya domin saukaka aikinsu.

Dangane da noma, Hon. Shuaibu Abdulrahman Adam ya bukaci manoma da makiyaya da su yi anfani da shirye-shiryen gwamnati na noma da kiwo, ciki har da rabon kayan noma, samar da wuraren kiwo da kuma ayyukan likitocin dabbobi.

Ya bayyana Funakaye a matsayin muhimmin cibiyar noma a Arewa maso Gabas, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya. Haka kuma ya yi kira ga Hukumar Lake Chad Basin da ta gina madatsar ruwa domin bunkasa noman rani a yankin.

Ya kuma buƙaci Hukumar Ilimi ta Jihar Gombe da ta tallafa wa karamar hukumar da kayan koyarwa domin kara inganta ilimi.

A ɓangaren matasa, shugaban ƙaramar hukumar ya yaba da shirye-shiryen bunkasa matasa, ciki har da horas da su sana’o’i da kirkirar cibiyar masana’antu ta Muhammadu Buhari Industrial Hub, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki.

Hon. Shuaibu Abdulrahman Adam ya bayyana Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda ƙoƙarinsa ya sa aka zabe shi a matsayin shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas da kuma na Arewa baki daya, yana mai yabawa rawar da yake takawa wajen magance matsalolin tsaro a yankin.

Haka kuma ya taya sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar murna tare da yi masa fatan alheri.

A karshe, ya buƙaci al’umma, shugabannin gargajiya da ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da marawa manufofin gwamnati baya, tare da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu da kuma yi wa jihar Gombe da Nijeriya addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya.

By ukarofi