Shugaban ƙaramar hukumar Gombe ya warkar da mahaukata takwas, yana fatan cigaba da shirin

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI

Shugaban ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani A.A. Haruna, ya ƙaddamar da shirin kula da lafiyar mahaukata a tituna, wanda ya kai ga warkar da mutum takwas.

A wata hira, Barista Sani ya ce shirin ya samo asali ne daga ƙudurinsa na rage yawan mahaukata a tituna ba tare da dogaro da tallafin ƙasashen waje ba. 

Ya bayyana cewa mutane takwas sun kwashe watanni uku zuwa shida suna jinya har aka mayar da su ga iyalansu.

Ya ce burinsa shi ne shirin ya zama abin koyi tare da haɗin kan gwamnati da sauran ƙananan hukumomi, yana mai cewa: “Ba wai yawan waɗanda aka warkar ba ne muhimmanci, amma nasarar gyara rayuwar mutum ɗaya ma babbar nasara ce.”

Barista Sani ya yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi su yi koyi daga wannan mataki.

Ya kuma ce shirin zai ci gaba da kasancewa cikin kasafin kuɗi na shekara-shekara don samun tsari mai ɗorewa.

Shugaban ya bayyana cewa sun kashe Naira 600,000 kacal wajen kula da waɗanda aka warkar, kuma yana fatan samun haɗin kai daga ƙasashen waje don faɗaɗa shirin.

By ukarofi