Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar BORNO, Babagana Umara Zulum, ya ci gaba da ziyarar al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa inda ya je garin Wulgo a ranar Talata.
Wulgo da ke gefen tafkin Chadi, a baya-bayan nan ne wasu mahara ɗauke da makamai suka kai wa hari, lamarin da ya tilastawa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa da ke kare garin ja da baya.
Ziyarar Marte, Kala-Balge, da kuma Wulgo, Zulum na da burin ganin an cimma matsaya guda a yaƙi da rashin tsaro da kuma ƙarfafa goyon bayan gida don samar da zaman lafiya da ci gaba.
A yayin rangadin, gwamnan ya tattauna da shugabannin yankin, inda ya saurari matsalolinsu.
Ya bayyana shirin ƙara kai kayan agajin jinƙai, da ƙarfafa ayyukan tsaro, da samar da kayayyakin ban ruwa na zamani da na gonakin damina domin sauƙaƙa farfaɗo da tattalin arziki a garin.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin shirye-shiryen jurewa da al’umma ke da shi tare da ƙarfafa gwiwar mazauna garin da su taka rawar gani wajen farfaɗo da garinsu.
“Na zo nan a yau don jajanta muku abin da ya faru a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
“Duk da ina ba ku ƙwarin guiwa da ku kasance masu juriya, ina so in tabbatar muku cewa gwamnatina ta himmatu wajen yin duk abin da za mu iya don ganin cewa garin bai zama kowa ba ko kuma Boko Haram ta ƙwace gabaɗaya,” inji Zulum.
