Neman gwal da muhimman ma’adanai ne ke ƙara rura wutar laifuffuka a Afirka – UNODC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ƙaruwar neman gwal da sauran ma’adinai na cigaba da rura wutar aikata laifuka da cin hanci da rashin kwanciyar hankali a nahiyar Afirka a cewar ofishin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da laifuka na Majalisar ɗinkin Duniya (UNODC).

Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoto UNODC ta fitar a ranar Talata a ɓienna, inda ta ce, nazarin da ta yi kan laifuffuka da ake fama da su na da alaƙa da neman gwal wanda ke assasa rikici a kan ma’adanai.

Sannan rahoton ya yi nazarin inda aka fi kai waɗannan ma’adanai da yin kasuwancinsu.

Rahoton ya ce, a yayin da mafi yawan gwala-gwalan ake samunsu a yankin Saharar Afirka da Latin Amurka da Caribbean da Kudu maso gabas na Asiya, wurin tace gwala-gwalan na yankin Turai ne da Asiya da Arewacin Amurka.

Nazarin ya kuma jaddada cewa akwai ƙungiyoyin da kamfanoni da wasu ɗaiɗaikun mutane da ke da hannu a ayyukan haƙo gwal ba bisa ƙa’ida ba da safararsa.

“A Afirka, akwai ƙungiyoyin da suke aikata laifukan da suka shafi harkar gwal kaɗai a yayin da wasu kan yi amfani da ribar da suke samu ta gwal wajen ɗaukar nauyin ta’addanci da ƙalubalantar mahukunta da rura wutar futina.”

Rahoton ya ƙara da cewa ƙungiyoyin da ke gudanar da irin waɗannan ayyukan na laifuka na yi ne saboda irin ribar da suke samu daga kuɗin gwal da ɗagawar darajarsa a kodayaushe.

Suna kuma sake zuba jari a harkar ayyukan ta’addancin a yayin da al’umma ke fuskantar cin zarafi da tursasawa wajen yin aiki da tilasta musu barin matsugunansu.

Rahoton ya ƙara da cewa ana kula da harkokin gwal ne saboda rage illar da yake da ita ga muhalli, sai dai masu yin haramtacciyar harƙallar na kauce wa bin matakan kariya da ake amfani da su kwata-kwata.

Sannan ya bayyana cewa haramtacciyar hanyar haƙar ma’adanai na ta’azzara matsalar muhalli da ya haɗa da amfani da sinadaran masu guba kamar Makyuri da sare bishiyoyi domin haƙar ma’adanai da zubar da datti ba bisa ƙa’ida ba.

Aikata hakan ya saɓa wa dukkan ƙa’idoji na kiyaye muhalli ba kuma illar haramtaccen haƙo ma’adanai ya tsaya ne ga shafar rayuwar halittu ba har ma da haifar da matsala da ke shafar lafiyar al’umma.

Rahoton ya nuna cewa ana tsallake iyakoki da ma’adanai masu darajar gaske kafin kai su inda za a tace su wanda ke ba wa ‘yan ta’adda da jami’an tsaro duka dama na tare irin waɗannan kayayyaki.

“ƙungiyoyin ta’addanci su ne suke shigo da haramtattun gwala-gwalai cikin kasuwa ta hanyar cin moriyar rashin kulawa da rashin adana bayani da giɓi da ake samu wajen sa-ido a yayin kasuwanci.

“Sai dai yadda wuraren tace gwala-gwalan suka cure a kusan yanki daya zai iya taimakawa wajen a datse harƙallar.”

“ƙara sa-ido zai iya taimaka wa wajen rage bazuwar haramtattun gwala-gwalai zuwa kasuwar duniya,” a cewar rahoton na UNODC.

By ukarofi