Daga GAMBO ISA a Abuja
Shugaban ƙaramar Hukumar Jakusko a jihar Yobe, Hon. Umaru Aguwa, ya yaba wa hukumar gudanarwa Jaridar Blueprint bisa karrama Gwamna Mai Mala Buni.
Idan dai za a iya tunawa, an zaɓi gwamnan ne tare da ba shi lambar yabo a matsayin Gwamnan Jaridun Blueprint na shekarar 2024 a wani bikin karramawar da aka yi kwanan nan a Abuja.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa Blueprint a ranar Juma’a, Aguwa ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a fannin ci gaban jama’a, samar da ababen more rayuwa, ilimi, ICT, asibitoci, bunƙasar tattalin arziki, tsaro da sauransu a matsayin wadanda za a iya tantancesu.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Salon jagoranci na Mai Mala, ya ƙarfafa aminci a dukkan ɓangarorin gwamnati kuma abin a yaba ne matuƙa.
“Daga gina hanyoyi masu inganci na ilimi/cibiyoyin ICT, ingantattun asibitoci da shirye-shiryen ƙarfafawa jama’a a faɗin jihar, nasarorin da ya samu ya wuce ɓangaranci har ya kai ga samar da ci gaba mai ma’ana a faɗin jihar Yobe.
“A ɓangaren kiwon lafiya, an samar da ingantattun kayan aiki na zamani a faɗin ƙananan hukumomin yankin 17.
