Gwamnatin Tarayya na barazanar korar ma’aikata 3,598 bisa gaza gabatar da takardun ɗaukar aiki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya guda 3,598 su na fuskantar barazanar kora saboda gaza gabatar da takardun ɗaukarsu aiki.

Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta umurci ma’aikata, waɗanda suka gaza zuwa a tantance su a 2021, su gabatar da kansu domin tabbatar da sahihancin ɗaukar su aiki.

An tsara tantance ma’aikatan daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Agusta, 2025, domin tabbatar da ingancin takardun shaidar ɗaukar aikinsu.

A cewar FCSC, duk wanda ya gaza halartar wannan tantancewa da aka shirya, za a ɗauka yana riƙe da jabun takardar ɗaukar aiki.

Hukumar ta umurci duka waɗanda abin ya shafa da su duba sunayensu a shafin intanet na FCSC, shafin intanet na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya, da kuma allon sanarwa na ma’aikatunsu.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce, “Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen gudanar da aikin sake tantance duk waɗanda suka gaza bayyana a lokacin aikin tantancewa na 2021.

“Waɗanda lamarin ya shafa suna cikin ma’aikatan da hukumar ta ɗauka daga shekarar 2013 zuwa 2020.”

Hukumar ta ƙara da cewa, duk ma’aikacin da ya gaza halarta, za a ɗauka yana da jabun takardar ɗaukar aiki kuma yana yin hakan ne da gangan domin guje wa tonon asiri.

Ana buƙatar waɗanda abin ya shafa su kawo takardun karatunsu na asali da kwafin su, ciki har da takardar ɗaukar aiki da ta ƙarin girma.

Haka nan kuma an buƙaci su je da takardar canjin matsayi, da kuma takardar albashi ta IPPIS na watan Yuli 2025.

Hukumar ta gargaɗi cewa ba za a sake ba da wani ƙarin lokaci ga waɗanda suka gaza halartar tantancewar a wannna karon ba.

Ma’aikatun da suka fi yawan waɗanda abin ya shafa sun haɗa da:

Ma’aikatar Yaɗa Labarai – ma’aikata 592

Ma’aikatar Ilimi – ma’aikata 506

Ma’aikatar ƙwadago – ma’aikata 440.

By ukarofi