
Shugaban Hukumar Raya Kogunan Haɗejia da Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan ceto ƴan makarantun nan da ƴan Bindiga suka sace a Jihohin Kebbi da Neja, inda shi shugaban ne kansa ya jagoranci ceto waɗannan ɗalibai cikin aminci.
A sanarwar daga ofishin hukumar, ta ce Alhaji Sulaiman Bichi ya kuma jinjina wa salon jagorancin Shugaba Tinubu saboda nuna damuwa kan abinda ya shafi tsaro da jin daɗi da walwalar al’ummarsa.
“Yana da matuƙar muhimmanci mu jinjina wa Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu saboda daukan matakan gaggawa dan ceto wadannan ya’ya namu. Yayin da tarihi ke nuni da gwamnatocin baya suka tsaya a matakin Allah wadai da kakkausar suka, Shugaba Tinubu a take ya fasa zuwa taro mai muhimmanci a Johannesburg ta Afrika ta Kudu domin shi da kansa ya jagoranci ceto wadannan Dalibai.”
Ya cigaba da cewa, wannan mataki da Shugaba Tinubu ya dauka na nuni da samun sabon sauyi a shugabanci”, inji Alhaji Bichi.
Haka kuma, Shugaban hukumar ya lura duk lokacin da masifa ta faru al’umma su kan nuna rashin jin daɗinsu da ɗorawa gwamnati laifi musamman Shugaban Kasa kan rashin daukan mataki ko halin ko in kula.
“Yana neman zama al’ada yayin da masifu suka faru ayi ta ganin laifin Shugaban Kasa kan sakacin sa ne yasa hakan ya faru. Sannan kuma Al’umma sukan gaza wajen yabo da jinjina yayin da aka sami nasara.”
“Shugaba Tinubu da Mai bashi shawara kan tsaro Mal. Nuhu Ribadu sun cancanci jinjina da yabo kan yanda suka nuna jarumtaka da sadaukarwa har aka kaucewa masifa aka ceto wadannan Dalibai cikin aminci da koshin lafiya.”
Alhaji Bichi ya bayyana cewa yayin da a tsarin dimokaradiyya Shugabancin na aiki ne domin hidimta wa al’umma, su cancanci a yaba musu duk yayin da sukayi abinda ya dace saboda su kara samun karfin gwiwa dasu da Hukumomin tsaro.
“Nasarar ceto waɗannan ɗalibai nasara ce ga Kasar mu kuma an sami wannan nasarar ne da Shugaban Kasa da kansa ya jagoranci wannan aikin da kuma jajircerwar jami’an tsaro. Ya kamata mu zama masu adalci da adawa mai ma’ana mu kasance masu yabawa da jinjina a lokacin da bukatar hakan ya taso. Yin haka zai bada hadin kai da samun nasara wajen kawo karshen matsalolin dake damun mu.
A ƙarshe, ya jaddada goyon bayan Hukumar domin samun nasarar manufofin Shugaba Tinubu musamman a fannonin samar da ayyukan ci-gaban ƙasa da tsaro a yankunan da ke ƙarƙashin ikonta.
