Sama da miliyan 100 za a raba wa ‘yan kasuwar Masaka da gobara ta shafa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Kwamitin da shugaban ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa barista Abubakar Aliyu Madaki ya kafa domin tantance lalacewa da kuma asarar dukiyoyi da aka yi sakamakon wata mummunar gobarar wuta da ta auku a kasuwar Masaka ta garin Karu din a bara ya gabatar da rahoton sa.

Kwamitin wadda ke ƙarƙashin jagorancin shugabanta wato Cif Mark Auta a yayin zaman ya kuma ba da wasu shawarwari na musamman dangane da yadda za a aiwatar da matakan hana wuta a kasuwannin domin hana irin wannan abin gaggawa sake faruwa nan gaba da tabbatar da tsaro a kasuwannin Karu baki ɗaya da sauran su.

Rahoton kwamitin wadda aka gabatar wa shugaban ƙaramar hukumar Karu barista Abubakar Aliyu Madaki a ranar talata na mako da ake ciki a sakatariyar ƙaramar hukumar.

A jawabin sa jim kaɗan kafin ya gabatar da rahoton a madadin kwamitin, shugaban kwamitin Cif Mark Auta ya bayyana cewa a yayin aiwatar da aikin nata kwamitin ya haɗa sunayen shaguna da mummunar lamarin ya shafa cewa sun kai shaguna da gine-gine dake kusa da kasuwar guda 993 inda aka yi rashin dukiyoyin kenan a taƙaice.

Shawarwari da shugaban kwamitin ya gabatar a yayin zaman sun haɗa da kan yin tsarin kasuwa da ya dace domin rage haɗarin hatsari da aka yi na aiwatar da matakan hana wuta a kasuwannin.

Yace kwamitin karkashin jagorancin nasa ya gudanar da tantancewar na gani da ido ne a yankunan da wutar ta shafa dama sauran kewayen kasuwar kuma ya gudanar da cikakken bincike ne da kuma aiki tsakani da Allah ba tare da nuna son zuciya ba, inda a ƙarshe ya kuma godewa shugaban ƙaramar hukumar game da wannan dama da ya basu.

A nasa jawabin bayan ya karɓi rahoton shugaban ƙaramar hukumar na Karu Barista Abubakar Aliyu Madaki ya bayyana godiya ta musamman na kwamitin saboda aikinsu na gaskiya kuma yayi alƙawarin ɗaukar matakai da suka dace nan da nan ba tare da ɓata lokaci ba don samun mafita a lamarin nan gaba.

Shugaban ya kuma sanar cewa za a rarraba sama da Naira miliyan 100, wadda gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya bai wa ƙaramar hukumar don tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa a kasuwar ta Masaka don rage musu asarar da suka yi ta gobarar.

Shugaban ya kuma gode wa gwamnan jihar ta Nasarawa saboda himmarsa wajen magance matsalolin ‘yan kasuwa a ƙaramar hukumar dama jihar Nasarawa baki ɗaya.

Suma a nasu ɓangaren da suke jawabi, wasu daga cikin mambobin kwamitin tantace ‘yan kasuwar waɗanda ke faɗa aji a Karu da jihar baki ɗaya da suka haɗa da tsohon shugaban ƙungiyar NURTW na jihar, Salihu Adamu da shugaban kasuwar Masaka, Danlami Salasi Gimba da kuma shugaban kasuwar Muhammadu Buhari ta ƙasa da ƙasa wato mista Rice Ahmed duk sun gode wa gwamnatin Karu ƙarƙashin jagorancin barista Abubakar Aliyu Madaki saboda ba su damar zama membobi a kwamitin inda suka kuma yi alƙawarin cigaba da naɗa nasu gagaruman gudumawa wajen cigaba ƙaramar ta Karu da jihar gaba ɗaya.

By ukarofi