Matakin da iyaye ya kamata su ɗauka ga ɗansu mai shaye-shaye

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Gabatarwa

Shaye-shaye (kamar amfani da tabar wiwi da ƙwayoyi da shisha da sauransu) ya zama barazana ga matasa a rayuwar yau. Wannan matsala ta zama ruwan dare a tsakanin matasa da yara ’yan shekara 13 zuwa 25. Lokacin da iyaye ko al’umma suka gano cewa, ɗansu ko wani yaro yana taɓa miyagun ƙwayoyi, da yawa su kan firgita, su yanke ƙauna ko su yi amfani da hukunci da duka da kyama da hantara da janye duk wani tallafi da suke ba shi, maimakon neman mafita mai kyau.

To, me ya kamata iyali da al’umma su yi da gaggawa bayan an tabbatar da cewa yaro yana cikin shaye-shaye? Wanne irin mataki ya dace?

1. Nutsuwa da kwantar da hankali 

Abu na farko shi ne kada a haukace ko a ɗaga murya. Iyayen da iyalai su zauna cikin natsuwa, su fahimci cewa yaron da ke shaye-shaye na bukatar taimako ba hukunci kawai ba. Da yawa daga cikin su suna shaye-shaye ne saboda wasu matsaloli da ba a gane ba – kamar:

i. Matsin lamba daga abokai (peer pressure)

ii. Matsalolin gida ko rashin kulawar iyaye

iii. Damuwar zuciya da rashin kwarin gwiwa ko Depression

iɓ. Sha’awar gwadawa saboda rashin sanin sanin illar yin hakan.

Waɗannan da ma wasu dalilai kan jefa yara shaye-shaye don haka iyaye ya kamata su ɗau mataki ta hanyar:

2. Tattaunawa Mai Ma’ana Da Yaron

Iyaye su zauna da yaron cikin tausa da kulawa, su fahimci yadda abin ya fara. Tambayoyi masu tausayi 

Wannan zai sa yaron ya buɗe zuciyarsa. Idan aka fara da fada ko tsawa, zai ƙaryata komai ko ya ƙi yin magana gaba ɗaya. 

3. Taimakon Gaggawa daga Masana da Likitoci

Shaye-shaye cututtuka ne a fannin ilimin lafiya da kwakwalwa (medical & psychological condition). Dole ne a nemi taimako daga:-

Likitan kwakwalwa (psychiatrist)

Masani kan shaye-shaye (addiction counselor)

Cibiyoyin warkar da masu shaye-shaye (Rehab Centers)

Akwai wuraren da ake kai yara domin horar da su, su warke daga shaye-shaye cikin kulawa, ilimi, da tarbiyya.

3. Gina Tsarin Kula da Yaro a Gida

Iyali su dawo da tsarin da zai taimakekkeniya da sa ido ga makwabta da abokanai da du wanda ya samu dama. Haka a lura da abokansa, da wa yake yawan zuwa wajensa? da kula da inda yake zuwa da lokacin dawowa gida.  Haka da kula da lafiya da  baccinsa da abincinsa.

4. Kada a Ware ko Tsangwamar Yaro

Da zarar an gano yaro yana shaye-shaye, wasu iyaye ko al’umma suna tsangwama, cin zarafi, ko wulakanci. Wannan yana ƙara dagula lamarin. Yaro zai ji an kore shi, ya fi karkata ga abokai masu shaye-shaye domin su ne kadai ke nuna masa “karɓuwa.” Wannan na iya jefa shi cikin muguwar  ƙungiyar ‘yan ta’adda ko manyan laifuka.

5. Ilimantar da Iyali da Maƙwabta

Baya ga kula da yaron, iyayensa, ‘yan uwansa, da makwabta su sami ilimi game da cutar shaye-shaye domin su fahimci halayyar masu fama da wannan matsala su guji yanke masa hukunci.

Su zama madogara wajen taimaka masa.

6.  Kafa Tsari a Makarantu da Masallatai 

Al’umma su tabbatar da cewa akwai

Horarwa a makarantu game da illar shaye-shaye

Koyi da dabi’un addini

Tattaunawa da malamai da limamai da shugabannin al’umma

Wannan zai taimaka wajen hana wasu yara su faɗa cikin wannan muguwar hanya.

7. Neman Taimakon Addini da Ruhi

Yaro ya kamata a kusa da shi da addini da Limamai ko malamai su yi masa nasiha cikin hikima. Tilas ko tsoro ba su da tasiri sosai, amma ilimi da gyara suna iya taimaka masa ya gane kuskurensa.

8. Tallafawa Yaron Ya Koma Rayuwa Mai Kyau

Bayan yaron ya fara janyewa daga shaye-shaye yana da kyau a tallafa masa ya shiga makaranta ko koyon sana’a da saka shi cikin taron alheri da kwararru. A saka shi cikin ayyukan al’umma don ya ji yana da muhimmanci. Wannan yana ƙara masa ƙarfi da kwarin guiwa, ya guji komawa baya.

9. Kula da Lafiyar Jiki da Tunanin Yaron

Shaye-shaye na iya barin lahani ga:

Hanta da Huhu da Kwakwalwa

Ido da fata

Halayya da tunani

Don haka a dinga kai shi asibiti akai-akai domin duba lafiyarsa da yi masa allura ko magani idan ya cancanta.

Kammalawa

Yaron da ke shaye-shaye ba dole sai an yi masa doka ko azaba ba. Mafi yawan lokuta, yana buƙatar ƙauna da kulawa da gyara da ilimi. Iyali da al’umma suna da rawar gani matuƙa. Idan aka mayar da hankali, shakka babu, yaro zai iya daina shaye-shaye ya koma cikakken mai amfani a cikin iyali da al’umma.

By ukarofi