Shugaban Kenya ya yaba da hanyar mota da kamfanin Sin ya shimfiɗa

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, aka fara aiki da tagwayen hanyar mota dake birnin Nairobi hedkwatar ƙasar Kenya a hukumance, wadda kamfanin shimfiɗa gada da hanya na ƙasar Sin wato CRBC ya zuba jari, tare da gina ta.

Shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya halarci bikin ƙaddamar da hanyar, inda ya yaba da yadda hanyoyin mota da kamfanonin ƙasar Sin suka shimfida, wajen magance matsalar cunkuson ababan hawa a birnin na Nairobi matuƙa.

A cikin jawabin nasa, Kenyatta ya ce, tagwayen hanyoyin na Nairobi da kuma sabuwar hanyar mota da ta kewaye gabashin Nairobi da aka kammala ginawa a ranar 31 ga watan Yuli, za su daidaita matsalar cunkuson motoci a birnin Nairobi matuƙa. Kafin fara aiki da tagwayen hanyoyin, sai an shafe aƙalla sa’o’i 3 a mota a wasu sassan birnin, amma yanzu mintuna 15 zuwa 24 ne kawai.

Shugaban ya ƙara da cewa, tun bayan gwada fara aiki da hanyar motar daga ranar 14 ga watan Mayu, hanyar ta taka rawa sosai, ta kuma taimakawa Nairobi shiga zamanin rage lokacin zirga-zirga, da ƙara yin mu’amala tsakanin mutane, da rage cunkuson motoci da inganta ayyuka.

Haka kuma ta samar da muhallin kasuwanci mai kyau, lamarin da zai ƙara samar wa Kenya damammaki a fannonin yawon shaƙatawa, da shirya tarurruka da sha’anin otel-otel.

James Macharia, ministan zirga-zirga da ababen more rayuwar jama’ar Kenya ya bayyana yayin bikin cewa, tagwayen hanyar mota dake Nairobi tana ɗaya daga cikin ababen more rayuwar jama’a mafi inganci a Afirka, kana kuma abin misali ne a fannin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin Kenya da kamfanoni masu zaman kansu.

Fassarawar Tasallah Yuan