Hollywood ta yi rashin babban jarumi, Paul Sorvino

Daga AISHA ASAS

Sharararren jarumi a masana’antar finafinai ta Hollywood ya cimma wa’adinsa, inda ya mutu yana da shekaru 83. Jarumin ya mutu ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a asibitin Mayo Clinic.

Labarin wanda ya fito daga ‘yar jarumin, Mira Sorvino ta bayyana mutuwar mahaifin nata a shafinta na tweeter, inda ta ke cewa, “mahaifina mai girma Paul Sorvino ya mutu. Zuciyata ta girgiza da rashin masoyin rayuwata. Kuma na tabbatar ƙarshen jin daɗi da soyayyarsa gareni ta zo ƙarshe. Uba ne nagari, Ina sonshi sosai. Zan yi ma ka aike da ɗaya daga cikin taurari a tafiyarka, mahaifina.”

Baya ga haka, jami’in hulɗa da jama’a na jarumin Roger Neal, ya bayyana wa manema labarai cewa, jarumin ya mutu ne a asibitin Mayo Clinic da ke Jacksonville, Florida. Inda ya bayyana cewar ya jima yana yaƙi da rashin lafiya.

Masana’antar ta Hollywood ta shiga alhinin mutuwar jarumin da ya taka muhimmiyar rawa a masana’antar. Tuni suka yi wa gawar rakiya cike da alhinin rabuwa da ɗan’uwan sana’a, kafin su ci gaba da nuna ƙuncin da kuma kewar jarumin a shafukansu na sada zumunta.