Hotunan tsiraici da Ranveer Singh ya yi sun bar baya da ƙura

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan hotunan tsiraici da shahararren jarumin masana’antar Indiya, Ranveer Singh, ya fitar, mutane da yawa daga ɓangarori da dama sun tofa albarkacin bakinsu, yayin da hakan ya janyo cece-kuce a ciki da wajen masana’antar, wasu na ganin rashin dacewar wannan tsiraici, yayin da wasu ke ganin hakan bai zama illa ba. Kasancewar hotunan na mujalla ne, hakan ya sa wasu ke ganin babu tsiraici a cikin abin da ya yi.

Wannan lamari dai ya sanya rabuwar kai a tsakanin jaruman masana’antar, inda wasu ke mayar da martani ga masu zagin abin da ya yi. Makusantan jarumin kamar, Arjun Kapoor ya bayyana abin a matsayin jarumta da ba kowa zai iya yi ba, kuma ya ƙara da cewa, a tsumayi zuwan nasa hotunan kwatankwacin na abokin nasa nan ba da jimawa.

Jaruma Priyanka Chopra ta bi layin masu yabo, inda ta kira bangon mujallar da aka sanya hoton nasa a matsayin “bangon mujalla mafi kyau da ƙasar nan ta tava gani.” Ita ma Masaba Gupta, ta bi bayan Priyanka Chopra da kalamanta kwatankwacin irin wanda ta yi. Ita kuwa Ram Gopal Varma cewa ta yi, “idan har mata na da damar yin gadara da kyawon surar jikinsu, su tallata ƙirarsu, me zai sa ya zama illa idan maza suka yi.”

Duk da cewa da yawa daga cikin manyan jarumai sun goyi bayan waɗannan hotunan, kuma sun bayyana su a matsayin marar aibu, ta hanyar wallafa wa a shafukansu na sada zumunta, kai har ma da waɗanda ke yin kwatankwacin hotunan suna yaɗawa. Sai dai hakan bai hana waɗanda ke kallon abin da muni faɗar albarkacin bakinsu ba. Da yawa sunyi tir da wannan aiki na jarumin tare da kiran haka a matsayin ɓata tarbiyya masu tasowa. Ciki kuwa har da wata hukuma ta FIR, wadda ta maka jarumin a kotu, inda ta kira hotunan nasa a matsayin ” wulaƙanta mutuncin mata.”

Jim kaɗan bayan maka jarumin kotu, jarumai masu goyon bayansa da kuma wasu masoyansa sun yin yi tir da wannan hukunci na FIR, inda suka dinga mayar da martani mai zafi. Jaruma Swara Bhasker, na ɗaya daga cikin waɗanda suka ga hukuncin a matsayin rashin yi wa jarumin adalci, kuma ta kira hukuncin a matsayin daƙushe hanyar samun aikin yi ga matasa marasa aiki.

A ‘yan kwanakin nan ne, jarumi Ranveer Singh ya yi wa wata mujalla aikin ɗaukarsa hoto, inda jarumin ya haska mujallar da surar jikinsa, cikin shiga wadda ba a saba gani ba. An ɗauki jarumin a yanayin da ya bayyanar da kusan duk illahirin surar jikinsa, idan ka cire al’urarsa, wanda hakan ya sava al’adar mujallun ƙasar.