MOPPAN ba ƙungiyar siyasa ba ce, masu amfani da ita a siyasa su daina – Al-Amin Ciroma

Daga AISHA ASAS

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya wato, MOPPAN ta gargaɗi masu amfani da ita wurin neman biyan buƙatunsu na siyasa, ta ja kunnen su da su daina amfani da sunanta yayin harkokinsu na siyasa. Gargaɗin ya zo ne a wata takarda ga manema labarai da Kakakin Al-Amin Ciroma, MOPPAN na ƙasa, ya rattaba wa hannu.

Al’Amin ya ce, “Ana jawo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki gami da shugabanni a matakin jiha da na ƙasa cewa, ƙungiyar MOPPAN ba ƙungiya ce ta siyasa ba, kuma ba ta da alaƙa da wata jam’iyya.”

Wannan tunatarwar tana zuwa ne a daidai lokacin da labarai suka zo wa shugabanni na ƙasa cewar wasu jihohi na amfani da inuwa gami da sunan MOPPAN wajen shiga harkokin siyasa a jihohinsu, wanda hakan, babban zunubi ne ga ƙungiyar da kuma masana’antar bakiɗaya. Hakan kuma yana rarraba kawunan ‘yan ƙungiyar.

Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya nuna takaicinsa ga masu irin wannan ɗabi’ar, ya kuma ja kunnen dukkanin waɗanda ke aikata hakan da ma masu tunani ko yunƙurin shiga harkokin siyasa da sunan ƙungiyar, su gaggauta janyewa daga aikata wannan ɗanyen aikin.

A ƙarshe, Dr. Sarari ya yi kira ga dukkanin shugabanni da membobi bakiɗaya da su mutunta martabar MOPPAN, su aikata abin da ya dace.