Waye Ibrahim Taiwo?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An haifi Ibrahim Taiwo a shekarar 1940, a ƙaramar hukumar Wushishi ta Jihar Neja da ke tarayyar Nijeriya. (Bincikenmu bai samo rana wata da kuma kwanan watan da aka haife shi ba). Ya taso a garin Kagara, har ma a lokacin da ya ke makaranta a kan kirashi da suna Ibrahim Kagara.

Ya yi Firamare ɗinsa a Senior Primary School Minna, sai kuma Bida Middle School. Ya halarci Provincial Secondary School da ke Okene na ɗan wani taƙaitaccen lokaci, inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare.

Aikin Soja:

Ya fara shiga aikin damara ne a shekarar 1961, inda ya halarci makarantar horar da sojoji da ke Kaduna. Sannan ya halarci makarantar Mons Officer Cadet School Aldershort. A lokacin da ya ke sansanin soji, ya yi aiki ne a matsayin jami’a mai kula da motoci sufuri, inda daya baya ya zama babban jami’i mai kula da motocin sufuri da sojoji, a Apapa Legas. Ya zama Staff Captain Army Headquarters a garin na Leges. Ya ƙara zama babban jami’i na 8 a garin Asaba, sannan babban jami’i na sufuri a Kaduna.

A lokacin yaƙin Biyafara shi ne shugaba a ɓangaren zirga-zirga da kuma rarraba sojojin yaƙi a kowane sansani na sojojin Nijeriya.

Rawar da ya taka a lokacin juyin mulkin Nijeirya a watan July 1966:

A lokacin juyin mulkin Nijeriya a shekarar 1966, wanda Chukwuma Kaduna Nzeogwu ya jagoranci sojoji, waɗanda mafi yawancinsu ’yan ƙabilar Ibo ne, juyin mulkin da a shi aka yi asarar rayukan manyan mutanen ƙasar nan, irin su; Sir Ahmadu Bello, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Samuel Ladoke Akintola, da kuma ministan kuɗi na wancan lokacin, wato Festus Okotie-Eboh, Ibrahim Taiwo shi ne kaftin na rundunar sojojin da aka ajiye don su bayar da tsaro a Yaba da ke Legas. A tare da shi akwai manya-manyan hafsoshin soji, waɗanda suka haɗa da: ƙaramin Laftanar Sani Abacha, Laftanar Muhammadu Buhari, Laftanar Ibrahim Bako, Laftanar kanal Murtala Muhammad, Manjo Theophilus Danjuma.

Waɗannan da ma wasunsu su ne suka taka rawar gani wajen ganin abinda ya faru bai faru ba a lokacin juyin mulkin na 1966. Saboda yadda suka nuna damuwarsu a zahiri da kuma baɗini ga yunƙurin sojoji bisa jagorancin Ironsi na hargitsa al’amuran mulki na wancan lokacin, wanda ya assasa juyin mulkin a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966.

Amma kash! Taka-tsan-tsan bata maganin ƙaddara.

A lokacin yaqin kuma Ibrahim Taiwo na daga cikin mutane uku jajurtattu masu aikin kwaso mutane daga garin na Asaba zuwa mafaka. Sun yi namijin ƙoƙari wajen bayar da kariya tare da kuɓutar da dubunnan mutane a ta’addancin garin Asaba, shi da Janar Murtala Muhammed, da Ibrahim Haruna. Shi ke kula da kuma tsara yadda aka kwaso dubunnan mutanen da ake zalinta a garin na Asaba, cikin nuna ƙwarewar aiki ta ban mamaki. Wannan aiki da ya yi ya sanya Nijeriya ta shiga cikin kundin tarihi na ƙasar da ta kware wajen iya kuvutar da ’yan ƙasa a lokacin yaƙin cikin gida.

Har ila yau, Kanal Ibrahim ya yi gwamnan jihar Kwara daga shekarar 1975 zuwa 1976.

Rawar da ya taka a lokacin juyin mulkin Nijeriya na shekarar 1975:

Taiwo ya taka muhimmiyar rawa a lokacin juyin mulkin da ya yi awon gaba da Yakubu Gowon sannan ya kawo Murtala Muhammad.
A ƙarƙashin aikinsa ne aka shigo da sojoji tare da rarraba musu wajen aiki. Sun yi wannan aikin kafaɗa da kafaɗa tare da Laftanar Kanal Muhammadu Buhari.

A ranar Laraba 30 ga watan July 1975 aka cire ƙarfin ikon mulkin da Janar Yakubu Gowon ke da shi, aka maye gurbinsa da Janar Murtala Ramat Muhammad, a wani juyin mulki mai kama da na ruwan sanyi. A ƙarƙashin kulawarsa, tare da aikin shigo da dakarun soji, gami da rarraba musu wurin aiki, shi da Muhammadu Buhari.

Mutuwarsa:

An kashe Kanal Ibrahim Taiwo ne a ranar Juma’a, 13 ga watan February 1976, a wani yunƙuri na hamɓarar da shugaban gwamnati na wancan lokacin, wato Janar Murtala Muhammad, juyin mulkin da Laftanar Kanal Buka Suka Dimka ya jagoranta, sai dai bai yi nasara ba. Amma a yunƙurinsa na kaucewa harin, wasu rukunin sojoji bisa jagorancin Dimka ɗin suka farfasa motar Murtala Muhammad, wanda ya yi sadaniyyar rasa ransa tare da na mai taimaka masa na musamman wato Laftanar Akintunde Akinsehinwa.

Kanal Ibrahim Taiwo ya rasu ya bar iyali, a ciki har da magajinsa a aiki, Birgediya Janar Ahmad Ibrahim Taiwo.

Ibrahim Taiwo na daga cikin mutanen da har yau har gobe wasu daga cikin ’yan ƙabilar Ibo ke matuƙar jin haushi, tare da farin cikin mutuwarsa, bisa zarginsa da su ke yi na cewa yana da hannu dumu-dumu wajen kashe ɗaruruwan mutane, ’yan ƙabilar Ibo ɗin, waɗanda basu ji ba basu gani ba a garin Asaba.

Tarihi ba zai tava mantawa da Kanal Ibrahim Taiwo ba saboda tasirinsa ga ’yan Nijeriya. Akwai tituna da dama da aka sanya wa sunansa a garuruwa mabanbanta a Nijeriya, misali: Ibrahim taiwo road Kano, Ibrahim Taiwo road Ilorin, da sauransu.