Ɗaukar nauyin iyali: Taimakon da ya wajaba a kan mace

Daga AMINA YUSUF ALI

Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata, mun tattauna a kan haƙƙoƙin iyali da kuma wasu dalilai da suke hana maza kasa sauke wannan nauyi da Allah ya raba ya ɗora musu. Su ma mata Allah ya ɗora musu nasu haƙƙoƙin.

Sai dai abin lura kusan dukkan ko ma dukka haƙƙoƙin da suka shafi ɗaukar nauyi ta fuskar kuɗi maza Allah ya ɗora wa. Sai dai wani lokacin maza kan bar wa mata wannan ragamar ba tare da tunani ko yardar ta ba. Wata kuma ba yardar tata amma ta karɓa don ba ta da zavi.

A halin yanzu, an shigo da wani salo na raba dai-dai tsskanin ma’aurata wajen ɗaukar nauyin gida. Amma abinda nake so mai karatu ya gane, akwai maslaha a wasu lokutan. Sannan kuma akwai taimakon da ya zama tilas mace ta yi wa namiji. Sai dai ba kowanne namiji ba, akwai mazan da suka cancanci wannan.

Rabe-raben maza dangane da ɗaukar nauyin iyali:

*Akwai namiji mai ko-in-kula: Wannan shi ne namijin da ba ruwansa da ɗaukar ɗawainiyar gida, sai dai abinda ya ga dama. Wani yana sana’a wani ba ya yi. Wanda ba ya sana’ar, ya dogara kacokam kan abinda matar take samu. Kuma da ma irin wannan sai ka ga Allah ya yi musu dace da samun jarumar mace jjirtacciya wajen neman kuɗi. Shi kansa nauyin kansa da kansa ma bai ƙi matar ta ɗaukar masa ba. Malalacin namiji kenan.

Wani kuma yana sana’ar amma ba zai yi wa iyalansa ba ne ba kawai. Ya zama abinda ake cewa inuwar giginya, na nesa ka sha ta. Iyalansa ba sa morarsa sai ‘yan waje. Sannan ba ruwansa da kyautata wa mace ko rarrashi. Ko kuma ya dinga kashe wa kansa kuɗin gabaɗaya, iyali ko oho. Musamman mai harkar matan banza ko shaye-shaye. Irin wannan namiji ba shi da tsoron Allah ko ilimin addini.

  • Sai na biyu, mai raba dai-dai: Shi wannan namiji shi ma ya kasu kashi biyu. Akwai mai wadata amma shi dole sai an raba ɗawainiyar gida tsakaninsa da matarsa. Yana ƙyashin ya ɗauki gabaɗya ɗawainiyar gidansa kamar yadda Allah ya umarce shi. Kuma wannan mutumin wataƙila matarsa tana da wata sana’a da take yi.

Yana ganin dole ta yi masa sakayya a kan damar sana’a da ya bar ta take yi. Ko tana so, ko ba ta so sai dai ya yi rabin hidimar gida ya bar mata rabi. Wani kuma kuɗinsu ne bai kai ba, sai dai ya yi wani abun. Ita kuma matar idan da dama ta yi wani. Irin waɗannan ba su fiye hana mata sana’a ba. Saboda sun fi kowa sanin amfaninta.

*Sai ɗan amana: Irin wannan rukunin maza ne idan za su tafi tsirara sai sun rufa wa iyalinsa asiri. Kuma ba banbanci da mai ƙaramar sana’a da mai babba, duk ɗaya. Su da ma ƙarfin halin a zuci yake ba na dukiya ba ne. Sukan hana kansu wani jin daɗin domin iyalansu su samu wadata. Komai wuya dole sai ya nema ya ba su.

Wacce hidima ce ta zama wajibi a kan mace?

Duk da mun san Musulunci ya ware wa mace haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanta a zaman aure, amma kuma akwai wasu lokuta da ya kamata mace ta shigo ciki ta taimaka. Kada namiji ya ɗauka kawai don mace tana aurenka ko don kun tara zuriyya, ko kuma don tana sana’a tana samu, a ce dole sai ta taimaka maka a kan ɗawainiyar gidan da Allah kai ya ɗora wa. Musulunci bai ce matarka ta yi maka komai ba sai don kyautatawa. Ko da Biloniya ce kuwa kai lebura, sai idan ta amince ta sarayar maka da haƙƙinta. Sai dai mata sukan taimaka wa maza idan buƙatar hakan ta taso.

A gaskiyar magana akwai maza ‘yan halas waɗanda ya dace mace ta tallafa musu da dukiyarta. Namijin da idan ba ta taimaka masa ba ma sai Duniya ta zage ta. Shi ne namiji ɗan amana. Wanda ta san dole fa sai dai idan ba shi da shi ne kawai abinda zai hana shi ya yi musu. To dole mace ta riƙe wannan alƙawari. Sannan akwai wanda ko ba shi da shi ɗin, ba ya ɗaukar nauyinsu, amma yana da mu’amala mai kyawun gaske. Yana girmama ta, yana kuma tausayinka da sauransu. Maza sun kasa gane kyawun mu’amala na sa mace ta sakar musu zuciyarta da dukiyarta gabaɗaya. Ba sai ka tursasa mace ba. A matsayinka na namiji idan kana kyautata mata ita ma za ta ji ta da zaƙuwa wajen son ganin ta kyautata maka.

Hakazalika, kamar yadda muka sani, mace ana gane alƙawari da biyayyarta ta ainahi ne a lokacin da namiji yake cikin talauci. Shi kuma namiji ana gane nasa yayin da yake cikin dukiya. Don haka, akwai juyin rayuwa, kuma abinda ka shuka, shi kake girba. Sannan ba kullum ake kwana gado ba. Allah zai iya ba wa namiji arzikin kuma daga baya ya karɓe kayansa.

To ka sani Yayana, irin yadda ka mu’amalanci matarka a lokacin da kake da kuɗi haka ita ma za ta mu’amalance ka lokacin da Allah mai kowa da komai ya juya lamarin. Domin Allah zai iya juya lamarin ya ƙwace arzikinka, ita kuma idan ya so ya yi mata arzikin. Don haka izina ce wannan ga maza da ma sauran mutane a kan wulaƙanta mutum saboda ka fi shi arziki. Kuma ko da Allah ya yi mata arzikin tana tallafa wa gidanka, kada ka yi tsammanin ma kuma za ta tallafa maka kuma ta cigaba da girmama ka a matsayin miji. Dole wani kaso na girmanka ya ragu idanunta.

Tsakanin Hausawa da sauran ƙabilu:

Kodayake, mai karatu zai ce to ai wasu ƙabilun suna yin raba dai-dai tsakaninsu da mijin wajen ɗaukar nauyin gida amma a bahaushiyar al’ada sai ya zama abin magana. Abinda da nake so a gane kowanne ɓangare da al’adunsu. Kuma al’adu abubuwa ne da aka riga aka karɓe su a kowacce al’umma.

Don haka, da ma duk al’umma mai raba dai-dai ta riga ta karɓe shi hannu bibbiyu kuma haka ake tun iyaye da kakanni. Shi kuma Bahaushe ya fi ɗora al’amuransa a kan koyarwar addini fiye da al’adu. Wannan shi ne dalilin da ya sa mata a ƙasar Hausa idan an bar musu nauyin gida suke jigata.

Saboda tun asali ma da ma ba su taso sun ga ana yi ba, kuma ba su saba ba. Sannan dalili na biyu, matan ƙabilu musamman Yarbawa da inyamurai da ƙabilun arewacin Nijeriya kamar Gwari da sauransu, an riga an raine su da koyon sana’a tun suna ƙanana sun saba dogaro da kansu ba da iyayensu ba. Sannan wasu ma su matan ke da alhakin noma da yin sana’a din tallafar gidajensu. Kuma sun taso sun ga iyaye da kakanni a haka.

To don sun zo gidan miji an yi raba dai-dai na wahalar gida ba za su girgiza ba sun saba. Haka su mazajensu na aure ba su ga illar fitar mace yin aiki ko sana’a a gida ko waje ba. Hasali ma sun ɗauke shi wani ɓangare na rayuwar yau da kullum.

Matansu har kasuwa suna zuwa su kasa kaya kamar maza. To mu kuma matanmu na ƙasar Hausa a gaskiya ba su taso da wannan aƙidar ba. Sun taso a gidajen da iyaye ke dogaro da iyaye maza, ta yaya za ka ce mata ita ta kula da nauyin gida a zauna ƙalau? Sannan idan ma suna son a yi raba dai-dan ai sai a zauna a yi yarjejeniya.

Wance zan bar ki ki yi sana’a amma za ki ɗauke kaza da kaza. Idan ta amince, shikenan. Idan ba ta yarda ba fa nauyin yana kanka kuma Allah zai hukunta ka idan ba ka sauke shi ba, ko ka tilasta mata ta yi wannan ɗawainiyar.

Shawara dai kawai maza su daure su sauke nauyin da Allah ya ɗora musu. A bar hangen abinda mace za ta yi. Ko ƙoƙarin hana ta haƙƙoƙinta saboda ƙyashi ko son azabtar da ita. Ka tuna fa ba don ita kake yi ba ko don halinta ko don ta isa ba. Kuma duk Duniya bayan iyayenka ba wanda suka fi sonka da buƙatarka kamar iyalinka.

Sannan kuma haƙƙin Allah kake saukewa, ba daɗi, ba ragi. Su kuma mata idan da hali a taimaka kamar yadda aka saba. Idan kuka kula duk yi wa kai ne. A dinga yi wa mazan da ba sa ɗaukar ɗawainiya nasiha saboda kada su sangarce nauyi gabaɗaya ya dawo kanku. Allah ya ba mu dacewa. Sai mako na gaba idan Allah ya kai rai.