HOTUNA: Yadda mawaƙi Rara ya shirya addu’ar zaman lafiya ga Nijeriya

A ƙarshen makon da ya gaba Shugaban tafiyar 13×13, mawaƙi Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya shirya addu’a ta musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassan Nijeriya.

Yayin taron, an gabatar da karatun Alƙur’ani da sauransu.

Taron addu’ar ya samu halartar n’manya da tsofaffin masu shirya finafinan Hausa na faɗin ƙasar nan, mata da maza.

Hoto: Sani Maikatanga Photography