Ta zuwa wa mijinta ruwan batir har lahira kan ƙarin aure

Wata matar aure ta halaka mijinta ta hanyar zuba mishi gubar asid saboda zai yi mata kishiya.

Matar ta yi wa mijin nata wanda suka shekara 12 tare wannan ɗanyen aiki ne ranar Lahadi a unguwar Apo da ke Masaƙa a Jihar Nasarawa.

Majiyarmu a yankin ta ce, a baya-bayan nan mamacin mai shekara 42, na yawan samun saɓani da matar tasa kan shirinsa na ƙara aure.

Majiyar ta ce, a baya matar ta taɓa kwashe kayanta daga gidan mijin na tsawon shekara biyar, daga baya shi kuma ya auri wata mata.

Wani qanin marigayin ya ce, “ɗan uwana na yawan yin ƙorafi kan matar tasa; wani lokaci ko abinci ba ta ba shi.

“Domin a samu zaman lafiya, sai ya nemi mu yi mata magana, mutane suka zo aka yi mata magana, amma ba ta ce komai ba.

“Ranar Lahadi sai muka ji hayaniya a gidan, sai muka garzaya muka shiga, ko da muka je sai muka samu ta riga ta yi mishi wanka da gubar asid, har jikinsa na zagwanyewa.

“Mun kai shi asibiti amma suka ƙi karɓar shi, shi ne muka kai shi wani wurin, daga baya ya rasu ranar Litinin da safe.”

Wani ɗan uwan mamacin ya ce, sun riga an yi mishi sutura bisa tsarin addinin Musulunci kuma sun shiga neman matar.

A wani labarin kuma daban, wata mata ta soka wa mijinta wuƙa har lahira a Adamawa.

Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta kama wata matar aure mai suna Caroline Barka, ’yar shekara 20, bisa laifin kashe mijinta, Barka Dauda, ​​da wuƙa har lahira.

Caroline Barka mazauniyar Angwan Tamiya ce a Ƙaramar Hukumar Madagali a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a jiya Asabar a Yola.

Ya bayyana cewa, ’yan sanda sun kama wacce ake zargin ne a ranar Juma’a, biyo bayan rahoton da aka samu daga wani ɗan uwan ​​marigayin.

“faɗa ne ya varke tsakanin wacce ake zargin, Caroline Barka, ’yar unguwar Angwan Tamiya, a ƙaramar hukumar Madagali, da mijinta mai suna Barka Dauda, ​ bayan da mamacin ya dawo gida a bige, sai ya faɗa kan jaririnsu ɗan shekara guda yayin da aka kwantar da shi a kan gado.

“wannan shaye-shayen nasa, da yawan yin dare da kuma rashin sauke nauyinsa a matsayin miji, shi ne ya fusata wacce ake zargin ta kama marigayin da kokawa har ta kai ga ta daɗa wa mijin wuƙa.

“Sakamakon haka ya faɗi a sume kuma daga baya aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa,” inji Nguroje.