Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban jami’in kamfanin mai na duniya, wato Shell, Wael Sawan, ya yaba wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wanda ya ce sun farfaɗo da kwarin gwiwar masu zuba jari tare da inganta yanayin kasuwanci a Nijeriya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Sawan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da suka yi da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cewar shugaban na Shell, kamfanin na ƙara zurfafa jarinsa a Nijeriya tare da haɗin gwiwar wasu abokan hulɗa, inda ya ce suna shirye su zuba ƙarin dala biliyan 20 sakamakon abin da ya kira hangen nesa da jagorancin Tinubu.
Ya ce, a halin yanzu Nijeriya ta zama ɗaya daga cikin wuraren da manyan kamfanonin mai da iskar gas na duniya ke son zuba jari, sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da aka samu.
Sawan ya bayyana wasu manyan ayyukan da Shell ke yi a ƙasar, ciki har da jarin dala biliyan 5 a aikin Bonga North, dala biliyan 2 a aikin HI, da kuma wasu ayyukan gas da ke da alaƙa da kamfanin Nigeria LNG.
A cewarsa, waɗannan jari-jari na nuna dogon shirin Shell na ci gaba da zama a Nijeriya, musamman ganin yadda tattalin arzikin ƙasar ke samun kwanciyar hankali idan aka kwatanta da shekarun baya.
“Jagoranci da hangen nesan ku sun samar da yanayin zuba jari da ya sa muka fifita Nijeriya a kan wasu ƙasashe,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, a yanzu kamfanoni na bai wa kwanciyar hankali na dogon lokaci muhimmanci fiye da sauye-sauyen siyasa na gajeren lokaci.
Sawan ya kuma bayyana cewa Shell ta ƙara yawan hannun jarinta a OML 118, wato Bonga Block, bayan ficewar kamfanin TotalEnergies daga aikin. A cewarsa, akwai yiwuwar aarin jarin dala biliyan 20 a aikin Bonga South West, wanda ya ce na daga cikin manyan ayyukan makamashi da ake sa ran za su fi girma a duniya.
Ya ce, kusan rabin wannan jari zai kasance kuɗin gine-gine da kayan aiki, yayin da sauran za su tafi kan ayyukan gudanarwa a cikin Nijeriya, lamarin da zai taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Shugaban na Shell ya bayyana sabbin matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka a matsayin wani sabon babi idan aka kwatanta da shekarun baya, lokacin da jarin waje a ɓangaren makamashi ke raguwa.
A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu ya amince da fitar da wasu keɓantattun tallafi da suka shafi zuba jari musamman domin aikin Bonga South West, inda ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, da ta tabbatar an kammala dukkan matakan doka cikin gaggawa.
Shugaban ya jaddada cewa tallafin ba na bai ɗaya ba ne, illa waɗanda aka killace kuma aka ɗaura su da sabbin jari da kuma ƙarin amfani da kayayyakin cikin gida.
Ya kuma bayyana fatansa na ganin an cimma matakin ƙarshe na yanke shawarar zuba jari a aikin Bonga South West kafin ƙarshen zangon mulkinsa na farko.
