Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 46 karo na farko cikin kusan shekaru takwas, wani ci gaba da ke nuna daidaituwar tattalin arziki da kuma kyakkyawan tafiyar da harkokin musayar kuɗaɗen waje a ƙasar.
Sabbin alƙaluman da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar zuwa ranar 22 ga Janairu, 2026, sun nuna cewa ajiyar ya kai kusan dala biliyan 46, matakin da ƙasar ba ta kai ba tun daga watan Agustan 2018 lokacin da ya tsaya a kusan dala biliyan 45.9.
Wannan ƙaruwa na zuwa ne sakamakon farfaɗowar da ta fara bayyana tun cikin shekarar 2025, abin da masana ke dangantawa da ingantaccen tsarin kula da kasuwar canjin kuɗi da kuma ƙoƙarin ƙarfafa garkuwar tattalin arziki. ƙarin ajiyar na nufin Nijeriya na da ƙarin damar biyan buƙatun shigo da kaya daga ƙasashen waje tare da tallafa wa daidaiton darajar Naira.
Alƙaluman sun nuna cewa ajiyar ya rufe shekarar 2025 a kusan dala biliyan 45.5, bayan da aka buɗe shekarar da kusan dala biliyan 40.8. Wannan ya nuna gagarumin sauyi idan aka kwatanta da farkon aiwatar da sabon tsarin kasuwar canjin kuɗi, lokacin da ajiyar ya taɓa sauka ƙasa da dala biliyan 40 sakamakon matsin lamba a kasuwa.
A watan Janairun 2026 kaɗai, ajiyar ya ƙaru da fiye da dala miliyan 500 cikin kwanaki 22, alamar da ke nuna cewa ana ci gaba da samun kwanciyar hankali a fannin. Tun daga tsakiyar watan Disambar 2025, ajiyar ke ci gaba da hauhawa a jere ba tare da tangarda ba.
Masana tattalin arziki na bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar masu zuba jari, tare da ba CBN damar tsoma baki a kasuwa idan buƙatar hakan ta taso domin kare darajar naira daga girgiza. A halin yanzu, ana kiyasin cewa ajiyar na iya rufe watanni kusan 15 na shigo da kayayyaki, ko kuma watanni 10 idan aka haɗa da hidimomi, abin da ya fi ƙa’idodin ƙasashen duniya na isasshen ajiya.
Haka kuma ana sa ran CBN zai sake fasalin manufofinsa na kasuwar canjin kuɗi a shekarar 2026, domin ƙara inganta tsarin da kuma daidaita kwararar kuɗaɗen waje. Bankin na hasashen ajiyar zai kai dala biliyan 51 kafin ƙarshen shekarar 2026, tare da dogaro da ƙarin kuɗaɗen shigar man fetur, yiwuwar fitar da takardun bashin gwamnati a kasuwannin waje, da kuma yawaitar kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙetare ke aikowa gida.
Bugu da ƙari, faɗaɗa matatar Dangote daga ganga dubu 650,000 a rana zuwa kusan ganga dubu 700,000, tare da burin kaiwa ganga miliyan 1.4 a nan gaba, na iya rage yawan shigo da man fetur daga waje. Wannan na nufin za a rage matsin lamba kan buƙatar dala wajen shigo da mai, lamarin da ka iya taimakawa wajen ƙara ƙarfin ajiyar kuɗaɗen waje.
