NDLEA ta kama ’yar Brazil da hodar iblis a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta sanar da cafke wata ’yar ƙasar Brazil mai suna Ingrid Benevides, mai shekaru 30, da ake zargi da shigo da hodar iblis mai nauyin kilo 30.09 ta hanyar ɓoye ta cikin buhunan kofi a Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama matar ne bayan ta iso Abuja ta jirgin ƙatar Airways, inda jami’an NDLEA suka daɗe suna bibiyarta ta hanyar bayanan sirri kafin su cafke ta.

Rahoton ya ce an ɓoye hodar iblis ɗin ne a cikin fakitocin kofi na kamfani da aka rufe da kyau, wanda a zahiri ya kamata su ƙunshi kofi, amma da aka buɗe su, sai aka gano farin sinadari da gwaji ya tabbatar hodar iblis ce.

Babafemi ya bayyana cewa jimillar hodar iblis ɗin da aka kama ta kai kilo 30.09, abin da ya sanya wannan kamen ya zama mafi girma da aka taɓa yi na hodar iblis a filin jirgin Abuja. An kiyasta darajar miyagun ƙwayoyin a kasuwar bayan fage ta haura naira biliyan uku.

A cewar NDLEA, a lokacin tambayoyin farko, matar ta ce ta shigo Nijeriya ne wai domin hutawa, amma bincike ya nuna cewa ta shigo ne da kayan da ake zargin na fataucin miyagun ƙwayoyi.

Bincike ya kuma nuna cewa Benevides na aiki a matsayin jami’ar tsaro mai zaman kanta a ƙasarta ta Brazil, lamarin da ya ƙara jawo hankalin jami’an bincike kan yadda ta shiga wannan harkar.

A wani ɓangare na daban, hukumar ta kuma kama wasu fasinjoji biyu a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas ɗauke da dubban kwayoyin tramadol da tapentadol da aka ɓoye cikin kayan abinci a jakunkunansu yayin da suke shirin tafiya Turkiyya.

Haka kuma, rundunar ruwa ta NDLEA ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da tabar wiwi nau’in “Ghana Loud” mai nauyin kilo 1,848 a bakin tekun Jakande da ke Lekki.

Hukumar ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da murƙushe masu safarar miyagun ƙwayoyi tare da kare al’umma daga illolinsu.

By ukarofi