2027: Sauya takara Musulmi daga Arewa zai iya jefa APC cikin haɗarin rasa mulki — Hannatu Musawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musawa, ta yi gargaɗi cewa jam’iyyar APC na iya fuskantar babbar barazana a zaben 2027 idan har ta yanke shawarar cire ɗan takarar Musulmi daga Arewacin Nijeriya a tikitin shugaban ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Musawa ta bayyana hakan ne yayin wata hira da aka watsa a wani shiri na siyasa, inda ake ta cece-kuce kan yiwuwar sauya tsarin tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya kai APC ga nasara a zaɓen 2023.

Ta jaddada cewa duk wani sauyi da zai kawar da Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ko wani ɗan Arewa Musulmi daga tikitin zai iya haifar da matsala mai girma ta fuskar siyasa.

A cewarta, tsarin siyasa a jihohin Arewa na da alaƙa sosai da asalin ƙabila da addini, lamarin da ke tasiri sosai ga yadda jama’a ke kaɗa ƙuri’a. Ta ce yankin Arewa ta tsakiya da ta yamma, musamman jihohi kamar Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Jigawa, Zamfara da Sakkwato, na da zurfin fahimtar siyasa kuma jama’a na ɗaukar zaɓe a matsayin wata dama ta nuna tasirinsu.

Musawa ta ce, duk wanda ke ganin za a iya sauya tsarin tikitin ba tare da sakamako ba, to bai fahimci haƙiƙanin siyasar Arewa ba. A ganinta, rashin wakilcin ɗaya daga cikin manyan rukunan Musulmi na Arewa a tikitin shugaban ƙasa na iya rage wa jam’iyyar karɓuwar da take da ita a yankin.

Game da yunƙurin ƙawancen jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027, ministar ta nuna kwarin gwiwa cewa Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Shettima na da cikakken ƙarfi da goyon baya domin neman wa’adi na biyu. Ta bayyana jam’iyyun adawa a matsayin masu cunkoso da manyan ‘yan siyasa da dama da ke neman gurbi ɗaya, lamarin da ka iya haddasa rarrabuwar kai.

Sai dai ta ce APC ba ta ɗaukar kowa da wasa, duk da cewa tana ganin yanayin da adawa ke ciki yanzu ba zai ba su damar kayar da shugabannin jam’iyyar a zaɓe mai zuwa ba. A cewarta, kasancewar adawa na da muhimmanci ga dimokuraɗiyya, amma APC na mai da hankali wajen ƙarfafa tubalinta da faɗaɗa goyon baya a sassan ƙasar nan.

Musawa ta jaddada cewa siyasa a Nijeriya na buƙatar fahimtar yanayin zamantakewa da tunanin al’umma, musamman a Arewa, inda tarihi da al’ada ke taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen shugabanni.

By ukarofi