Shugabancin Majalisa ta 10: Tinubu zai gana da zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Tarayya na jam’iyyun hamayya

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa ranar Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, zai gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisun taraya na jam’iyyun hamayya domin cimma daidaito dangane da shugabancin Majalisar Tarayya.

Zaɓaɓɓun sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai na jam’iyyun hamayya da suka haɗa da PDP, Jam’iyyar Labour, NNPP da sauransu, na daga cikin waɗanda Shugaba Tinubun zai gana da su.

Majiyarmu ta ce, za a yi zaman ne ranar Litinin, 5 ga Yuni a Fadar Shugaban Ƙasa tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 5:00 na yamma.

Takardar gayyatar wadda majiyarmu ta samu leƙawa, na ɗauke ne da sa-hannun Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, Tijani Umar, a madadin Shugaban Ma’aikatan Fadar, Femi Gbajabiamila.

An ce sanatoci za su fara ganawa da Tinubu da misalin ƙarfe 3:00 na rana, sannan ‘yan Majalisar Wakilai da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

Duk da dai takardar gayyatar ba ta bayyana batutuwan da za a tattauna yayin taron ba, amma ana kyautata zaton batun shugabancin Majalisa ta 10 na daga cikin muhimman abubuwan da ganawar za ta maida hankali a kai.