Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati, EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kakkausar suka ga fastoci da limamai, inda ya ce wasu daga cikinsu sun fi jami’an gwamnati cin hanci da rashawa.
Olukoyede, wanda ya yi magana a wani taron shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da aka gudanar a Legas ranar Juma’a, ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC ta ƙwato miliyoyin Naira daga hannun wata ƙungiyar addini kwanan nan.
Ya ce, “Bayan naɗi na, na yi tunani a kan matsayina na shugaban hukumar da sakatariyar hukumar. Na gane cewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen mu shi ne kare mutuncin Nijeriya. Ba tare da gaskiya ba, rashawa yana bunƙasa. Na tambayi kaina, ta yaya zan iya yin bambanci?
“Mataki na farko da ba a taɓa yin irinsa ba shi ne na bayyana kadarorina a bainar jama’a, tare da kafa wani sabon tsari. Ba wanda ya umarce ni; sadaukarwa ce ta sirri don nuna gaskiya. Na ƙalubalanci kowane ma’aikacin hukumar da ya yi haka saboda adalci yana buƙatar hannu mai tsabta.”
A cewarsa, duk da matsin lamba da aka yi masa, ya bi doka, ya kuma yi watsi da buƙatun da ba su dace ba, har ma daga masu faɗa a ji.
“Ko da yake an gargaɗe ni matsayina na iya kawo cikas ga burin wasu, amma na tsaya tsayin daka. Imani na ya samo asali ne daga bin gaskiya ga ƙa’idoji da kuma imani da manufa mafi girma fiye da yanayin yanzu.
“Wasu abubuwan da muke yi da za su iya kawo mana cikas, za mu gudu daga gare su. Don haka, makonni uku bayan an kafa kwamiti, tabbas, wasu daga cikinmu da suka bi abin da ya faru a farkon shekarar 2020, ciki har da ku, sun fahimci abin da nake magana a kai — suna na ya kasance ko ina, hagu, dama, da kuma tsakiya.”
Olukoyede ya ce ana bincikensa tsawon shekaru biyu da rabi kuma an dakatar da shi saboda bai yi komai ba. A ƙarshen ranar, ya ce an ba shi takardar kuɗi mai tsoka.
“Don haka, idan kana nan, kai jami’in gwamnati ne, kana riƙe da muƙamin amana, ka sani wata rana za a tambaye ka kan abin da ka aikata. Idan ba a nan duniya ba, to can lahira,” in i shi.
Ya yi nuni da cewa ba da jimawa ba ya dawo a matsayin shugaban wannan hukuma inda aka yi masa ba’a kafin a same shi da tsafta.
Ya ce, “Na gane cewa akwai manyan fastoci da yawa a nan, iyayenmu maza da mata, shugabannin masana’antu. A cikin aikina a cikin yanayin yaƙi da cin hanci da rashawa, na sami dalili na yanke hukunci ga fastoci.
“Ba labari ba ne mai daɗi, amma ina so in gaya muku cewa na sami dalilin da zai sa na yanke wa limamai da sauran shugabannin addini hukunci.”
“Don kawai ana kiran wani Fasto, Kirista, Musulmi, ko Imam ba ya hana su cin hanci da rashawa.
“Abin baƙin ciki ne cewa ɗaya daga cikin fastocin da muka yanke wa hukunci ɗan coci na ne. Haka ne, yana iya zama ba labari mai daɗi ba ne a faɗi, amma gaskiya ne.
“Muna iya tsayawa a nan mu yi magana na nahawu daga safe zuwa maraice, amma wannan ba yana nufin muna da tsabta ba. A halin yanzu, waɗannan mutane ne da ke da matsayi na gaba a cikin cibiyoyin addini. “
Ya ce a wasu ƙasashe, mutane ba sa taruwa a coci ko masallatai don yin addu’a sau biyar ko goma a rana. Ya ce, “Ba su ma san Yesu Kiristi ko Annabi Muhammad ba, amma suna yin abin da ya dace. Suna bin doka, suna bin ƙa’idoji, suna bin doka.
“Mu duba kanmu. Da gaske mu masu tsoron Allah ne? Shin mun fahimci abin da ake nufi da zama Kirista ko Musulmi, ko kuwa muna yin addini ne kawai?
“Mu da ke kan gaba a wannan yaƙin, idan muka yi motsi ɗaya ko biyu, mutanen da ya kamata su ba mu goyon baya sun fara jefa kalamai a shafukan sada zumunta. Duba, ba abin kunya ba ne? Haka ne, ba mu kamiltattu ba ne, amma idan muka ga wani abu da zai kai ga yin abin da ya dace, bai kamata mu goyi bayansa a matsayin mutane masu tsoron Allah ba?
“A wata jiha, mun gudanar da wani aiki. Mun kama mutane 227. Kamar yadda nake magana da ku, an gurfanar da 113. Na riga na shigar da ƙara a kan fiye da 80.”
Ya ce a cikin ƙanƙanin lokacin da ya ke kan karagar mulki, ya samu dalilin gurfanar da wasu tsofaffin gwamnoni biyu a gaban kotu bisa laifukan damfara da suka kai biliyoyin Naira, ya kuma ba da shawarar a dakatar da wasu mutane daga aiki.
