Shuwagabanni masu goyon bayan Ukraine za su yi taro ta yanar gizo

Spread the love

Fadar shugaban ƙasar Faransa ta tabbatar cewa gungun ƙasashen da ake kira Coalition of the Willing — ƙungiyar da ke ba Ukraine cikakken goyon baya — za su gudanar da wani taro a ranar Alhamis mai zuwa ta hanyar bidiyo.

Taron, wanda Birtaniya da Faransa ke jagoranta, zai samu hallarar shugaban gwamnati na Birtaniya Keir Starmer, da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy. Downing Street ta tabbatar da shiga taron.

Zelenskiy ya ce Ukraine na shirin gudanar da tattaunawa da jami’an Amurka kan batun sake gina ƙasar da ci gaban tattalin arziki, a wani ɓangare na shirin zaman lafiya da Rasha.

By ukarofi