Netanyahu zai gana da Trump kan mataki na biyu a shirin Gaza

Spread the love

Firaminista Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa mataki na biyu na shirin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Gaza ya kusan kaiwa ga aiwatarwa, duk da cewa akwai muhimman batutuwa da ba su warware ba — musamman batun ko za a tura sojojin ƙasashen duniya a matsayin dakarun tsaro a Gaza.

Netanyahu ya faɗi haka ne yayin taronsa da Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, a birnin Urushalima. Ya ce zai gudanar da muhimmiyar tattaunawa da Shugaban Amurka Donald Trump a ƙarshen wata domin tabbatar da yadda mataki na biyu zai tabbata.

Fadar Firaminista Isra’ila ta tabbatar a ranar 1 ga Disamba cewa Trump ya gayyaci Netanyahu zuwa Fadar White House, ko da yake ba a bayyana ranar ziyarar ba.

Netanyahu ya ce zai tattauna da Trump kan yadda za a kawo ƙarshen mulkin Hamas a Gaza, inda ake ci gaba da samun zargin karya yarjejeniyar tsagaita wuta daga ɓangarori biyu tun bayan da ta shiga wata na biyu.

A mataki na farko na shirin Amurka, Isra’ila ta ci gaba da riƙe kashi 53% na Gaza, tare da musayar fursunoni tsakanin ɓangarorin. Har yanzu ana jiran mika gawar wani jami’in ’yan sandan Isra’ila da aka kashe a harin 7 Oktoba 2023.

A mataki na biyu na shirin, Isra’ila za ta janye daga wasu yankuna, a kafa hukumomin wucin gadi a Gaza, a tura dakarun ƙasashen duniya, sannan a fara makaman kashe ƙungiyar Hamas da gina Gaza.

Merz ya ce Jamus za ta taimaka wajen sake gina Gaza, amma tana jiran sakamakon ganawar Netanyahu da Trump don sanin yadda Amurka za ta taka rawa. Ya jaddada cewa mataki na biyu “ba zai jinkirta ba”.

A gefe guda, duk da tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-haren sama, wanda ta ce domin kare kanta. Hukumar lafiya ta Gaza ta ce mutane 373 suka mutu tun bayan tsagaita wuta, yayin da sojojin Isra’ila uku suka rasa rayukansu.

Netanyahu ya ce zai tattauna da Trump kan yiwuwar zaman lafiya da ƙasashen Larabawa da ma dai Falasɗinawa, amma ya jaddada cewa Isra’ila ba za ta taɓa barin ikon tsaron Yammacin Kogin Jordan ba.

Ya kuma bayyana cewa “batun haɗa yankin” (annexation) na Yammacin Kogin Jordan har yanzu ana ci gaba da tattaunawa — duk da cewa Trump ya shaida wa shugabannin Musulmi cewa Isra’ila ba za ta aiwatar da hakan ba.

By ukarofi