Sojin sama na Nijeriya sun kashe mayaƙan ISWAP a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) ta gudanar da hare-haren sama kan mayakan ƙungiyar ISWAP a ƙauyen Aduwa, ƙaramar hukumar Guzamala ta Jihar Borno.

Rahotanni sun ce hare-haren, waɗanda aka kai ranar 21 ga Agusta, 2026, sun hallaka wasu mayakan ISWAP tare da lalata motocin yaƙi guda biyu na ƙungiyar.

Zagazola Makama, wata kafar yaɗa bayanan yaƙi da ta’addanci, ta ce bayanan sirri sun nuna cewa hare-haren sun yi tasiri sosai, inda dukkan mutanen da aka gani a wurin da aka kai harin aka tantance su a matsayin mayakan ISWAP.

A cewar rahoton, ɗaya daga cikin motocin yaƙin da aka lalata ta ƙone ƙurmus yayin harin.

Bayan harin, an ga wasu daga cikin mayakan da suka tsira suna ƙoƙarin kwashe waɗanda suka jikkata daga yankin, yayin da wasu kuma ke jan wata mota da ta lalace zuwa wajen Gudumbali, da alama suna kan hanyar zuwa yankin Tafkin Chadi.

Rahoton ya ce ana ganin wannan yunƙuri na daga cikin matakan da mayakan da suka tsira ke ɗauka domin ceto waɗanda suka jikkata da kuma ficewa daga yankin da aka kai harin.

Sai dai ba a tabbatar da adadin mayakan da aka kashe ko suka jikkata ba, yayin da ake ci gaba da tantance ko wasu manyan kwamandojin ISWAP na cikin waɗanda aka hallaka.

An bayyana cewa ƙarin binciken illar da harin ya haifar da tattara bayanan sirri za su taimaka wajen gano ainihin adadin waɗanda abin ya shafa.

By ukarofi

Leave a Reply