Sojoji sun ƙwato babura 17 da makamai bayan daƙile harin Lakurawa a sansanin Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar daƙile wani harin sanyin safiya daga wasu mutane da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne a sansaninsu na Forward Operating Base da ke yankin Maiyama a Jihar Kebbi, inda suka ƙwato babur guda 17 bayan maharan sun janye farmakin nasu, kamar yadda mahukuntan soji suka faɗa.

Al’amarin ya auku ne a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026 a lokacin da wani dandazon ‘yan ta’adda da ya ƙunshi sama da babura 100 ya afkwa wa yankin sansanin tare da buɗe wuta, a cewar sashen Atisayen FANSAR YAMMA. Rundunar Sojin ta ce maharan sun je yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai ciki har bindigogi masu jigida da makami mai linzami.

Dakarun Sashe na 2 na jami’an haɗaka na JTF a Areaa maso Yamma ne suka mayar da martani wanda hakan ya tilasta wa maharan janyewa kafin su cimma manufarsu. A yayin da suke ƙoƙarin tserewa, maharan sun zubar da makamai da wasu kayayyaki, inda sojoji suka kora su tare da cigaba da kutsawa a dazukan kewayen yankin.

A sanarwar da fitar, rundunar sojin ta ce jami’anta sun ƙwato babura 17, bindigar PKT machine gun, AK-47 guda, tarin alburusai da wata na’urar sadarwa da ake zargin an yi amfani da ita yayin farmakin. Ƙwato waɗannan ababe ka iya rage ƙarfin maharan wajen cigaba da gudanar da miyagun ayyukansu a yankin, kamar yadda sojin ta bayyana. Ta ƙara da cewa, jami’ai suna cigaba da sintirin bincike da ƙoƙarin farauto ‘yan ta’addar da cigaba da bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya a shiyyar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply