Daga UMAR GARBA a Katsina
Sojojin runudar Operation FANSAN YAMMA sun ceto ɗaliban jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-Ma guda shida tare da direbansu da ’yan bindiga suka yi garkuwa a Jihar Katsina.
An kuɓutar da ɗaliban waɗanda dukkansu mata ne tare da direban nasu a hanyar Dayi-Malumfashi da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Jihar Katsina.
Sanawarar da mai magana da yawun rundunar, Laftanar-Kanar Aliyu Ɗanja, ya fitar a ranar Talata ta ce, an ceto ɗaliban tare da direban motar hayar da suka hau ne a ranar Litinin, 21 ga watan nan na Satumba, 2026.
Ya bayyana cewa an yi nasarar kuɓutar da su ne bayan sojojin sun samu kiran neman ɗaukin gaggawa game da wata motar haya da aka kai wa hari a kan hanyar ta zuwa Katsina daga Kaduna.
Laftanar-Kanar Ɗanja ya bayyana cewa martanin gaggawa da sojojin suka kai ya tilasta wa masu garkuwa da mutanen tserewa inda suka bar mutanen da ke hannunsu.
Ya ce duka mutanen da ke cikin motar an ceto su ba tare da sun samu wata matsala ba, kuma an tantance bayanansu da yanayin lafiyarsu kafin aka miƙa su ga hukumomin da suka dace domin damƙa su a hannun iyalansu da hukumomin makarantarsu.
