Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun Operation Delta Safe na rundunar sojin Nijeriya da ta mayar da hankali wajen daƙile satar man fetur da kuma tabbatar da tsaro a yankin Neja Delta, sun daƙike satar ɗanyen mai da aka kiyasta kuɗin ta ya haura Naira Biliyan 1.93 cikin mako guda.
Daraktan Ayyukan Yaɗa Labarai Na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ƙara da cewa, aikin ya kai ga kwace litar ɗanyen mai lita 1,009,733, lita 304,811 na gas, lita 3,480 na Kalanzir, lita 19,875 na Man Fetur, Injiniya masu ɗaukar 6.0 na tace mai.
“Bugu da ƙari, sojoji sun lalata kayayyakin aikin tace ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka haɗa da babban tukunya mai ɗaukar lita 351, da ramukan tace mai 418, jiragen ruwa 30, tankunan ajiya 160, ganguna 721, da haramtattun wurare tace mai 95,” inji shi.
A wani ɓangare na ayyukan tsaro a faɗin ƙasar, ya ce sojoji sun kama mutane 430 da ake zargi da aikata laifuka da suka haɗa satar mai, da ‘yan ta’addanci, garkuwa da mutane, da sauran abubuwan da ke kawo cikas ga tsaron ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa, a tsawon lokacin da ake binciken an ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, yayin da ‘yan ta’adda 204 da ‘yan uwansu suka miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Kangye ya jaddada jajircewar rundunar sojin ƙasar wajen kare martabar yankunan Nijeriya.
