Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Ƙungiyar masu dillanci da bada hayar gidaje, filaye da gonaki da sauransu ƙarƙashin shugaban ta na ƙasa, Alhaji Musa Khalil Hotoro ta shirya gagarumin taronta na ƙasa a Kano a ranar Asabar da ta gabata.
Taron wanda ya samu halartar shugabanin ƙungiyar ta Property Agents & Landlord Association of Nigeria (PALDAN) daga jihohin Nijeriya kamar dai yadda shugaban ƙungiyar na ƙasa ya bayyana a wannan gagarumin taron da ya gabata a birnin Kano.
A jawabinsa, shugaban ƙungiyar na ƙasa Alhaji Musa Khalil Hotoro ya bayyana cewa wannan ƙungiya mai ɗimbin albarka ta hanyar samama matasa da manya maza da mata ayyuka an kafata ne domin kishin ƙasa da gina ƙasa wanda kuma tana bada gagarumin gudunmawa sosai wajen samawa ɗimbin al’ummar Nijieriya aiki tun daga kan matasa da suka kammala makarantu a matakai daban-daban da ‘yan kasuwa da suka ajiye kasuwanci sai tsofaffun ma’aikata da suka kammala aiki da sauran masu sana’o’i da suka zaɓi cewa wannan sana’a ta dillanci ta fi musu sana’o’i da suka baro a baya.
Hakan ce ta sa ɗimbun miliyoyin mutane suka samu aiki a wannan ƙungiya wacce hakan yake kawo cigaban tsaro, zaman lafiya, buƙasar tattalin arziki da sauransu a Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.
Daga ƙarshe akwai kaɗan daga cikin ɗimbin shugabannin ƙungiyar da suka zo daga jihohi da dama ne suka yi jawabin yadda suke gabatar da ayyukansu a ƙungiyance da akwai Alhaji Shafiu wanda aka fi sani da Kwamanda shugaban PALDAN na Kaduna ya bayyana cewa ƙungiya akwai arziƙi mai tarin yawa a wannan sana’a kuma a Kaduna ya ce kashi 90 cikin 100 na matsaloli da rigingimun filaye a kotuna ƙungiyar ta magance su sakamakon tsare-tsaren da ƙungiyar ke aiwatarwa.
Sai kuma shugaban PALDAN na jihar Taraba Hon. Musa Abdu Danburandin Muri ya bayyana cewa tsarin ƙungiyar a Taraba ya haɗa kai da ɗaukacin jami’an tsaro na Njieriya domin tsarkake sana’ar da ake samun arziki fiye da ko wacce sana’a mudun ansa gaskiya da amana a sana’ar kuma wannan tasa suma kashi 80 na ƙararraki da ake kaiwa kotu na da alaƙa da filaye ko gonaki amma tsarin da suka yi a Taraba ya zaftare kashi 80 cikin 100 na ƙarrarki na filaye a Taraba.
