
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun haɗaka na Atisayen FANSAN YAMMA a Arewa maso yammacin Nijeriya, sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargin abokin hulɗar ‘yan ta’adda ne mai samar musu da wasu ababen amfanin yau da kullum.
Haka kuma, sun samu tsabar kuɗi a hannunsa da adadinsu ya kai kimanin Naira miliyan 5.302, sannan kuma suka katse wani abin fashewa (IED) da aka dasa a wata babbar hanya a Jihar Zamfara.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar FANSAR YAMMA, Laftanal Kanal Aliyu Ɗanja ne ya bayyana haka a wata takarda a ranar Juma’a, inda ya ce an gudanar da atisayen ne a ranar 7 ga Agusta a wurare daban-daban a sassan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kuma farmaki ‘yan ta’adda a mafakarsu da ke ƙananan hukumomin Zurmi, Birnin Magaji da Shinkafi, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin jeji.
A cewar Laftanal Kanal Ɗanja, jami’an sashe na 2 da ke aiki da tawagar lalata ababen fashewa (EOD) na ‘yan sanda sun yi nasarar lalata wani bom da aka dasa a kusa da ƙauyen Jabanda da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi.
Ya ce, a yayin dawowa daga wannan atisayen ne dakarun suka yi arangama da wasu ‘yan ta’adda a ƙauyen Birnin Tsaba da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji, lamarin da ya yi sanadiyyar musayar wuta da ya kai ga ‘yan bindigar sun ja da baya tare da tserewa zuwa jeji mafi kusa. A yayin bincike, sojojin sun samo babura biyu, hular sojoji, ƙaramin rediyo da wasu ababe.
A Ƙaramar Hukumar Shinkafi dakarun Sashe na 2 da ke aiki tare da ‘yan sanda Mobile Squadron sun yi ba-takashi da ‘yan ta’adda a yankin Kwanar Jolof bayan samun wani bayani na sirri, inda suka tilasta musu tserewa. Bayan haka ne aka samo babur, kakin soja, rigar ciki, hula mai malafa da wasu ababe da ‘yan ta’addar suka watsar yayin tserewar.
A wani labarin kuwa a yayin sintiri a Maradun, dakarun tsaro sun kama wani mai shekara 35 da ake zargi da yi wa ‘yan ta’adda aiki mai suna Lawali Ɗan Alo. A yayin binciken jakarsa, an samu kayan abinci, wayar hannu da kuma tsabar kuɗi na Naira miliyan 5.302.
