Sojoji sun yi nasarar hallaka wani babban kwamandan Boko Haram Abu Rajab da wasu mutum biyu a wani sumame da suka kai dajin Sambisa.
Wannan samamen ya samu haɗin gwiwar ‘yan sakai inda ya faru a wani sansani na ‘yan ta’addan da ke Bula Daloje, a ƙaramar hukumar Bama.
Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan yayin da suka kashe uku daga cikinsu, yayin da saura suka tsere.
A cikin waɗanda suka kashe akwai wani babban kwamandan ƙungiyar Abu Rajab wanda an jima a na neman shi. Sun yi nasarar ƙwato bindiga ƙirar Ak47 da wayoyin hannu da dama.
