
Daga NASIR S. GWANGWAZO
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen kungiyar ECOWAS su amince da kuma aiwatar da daftarin yarjejeniyar yaƙi da cin hanci da rashawa.
A yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 6 na Ƙungiyar Taron-Dangin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Yammacin Afirka (NACIWA) a Abuja, Tinubu ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai da zaƙewa a yayin yaƙi da cin hanci da rashawa da ke addabar yankin.
Shugaban wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya sanar da bayar da gudummawar ginin ofishin dindindin ga hedikwatar kungiyar ta NACIWA, kana ya buƙaci ƙasashen mambobin ƙungiyar da su bari a ga yaƙin a aikace maimakon a takarda, sannan su mai da hankali kan bin ka’idojin shari’a da inganta haɗin-gwiwar ƙasa da ƙasa, tare da baza gaskiya a fai-fai ga al’umma a yayin yin amfani da albarkatun kasa ko sayo kayayyakin gwamnati.
Shugaba Tinubu ya bayyana illolin cin hanci da rashawa, da cewa wata cuta ce mai karya garkuwar zamantakewa ta hanyar cin amanar jama’a, da gurgunta rarraba albarkatun kasa cikin adalci.
Don haka a cewarsa , Najeriya ta shirya tsaf don tabbatar da samun nasarar NACIWA a yankunan ECOWAS a babban shirinta na yaƙi da cin hanci da rashawa .
Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama da suka haɗa da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; da Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Mista Ola Olukoyede.
