‘Yan bindiga sun saki bidiyon basaraken Jihar Sokoto ɗaure cikin jini

Spread the love

A wani faifan bidiyo da ya ke yawo wanda mai garin Gatawa Muhammad Bawa, yayi kira da gwamnatin Jihar da ta kawo masa agaji a hannun ‘yan bindiga domin wa’adin da su ka bayar ya wuce.

A faifan bidiyon, an nuna mai garin ɗaure cikin jini. mai garin ya kwana 22 kenan a hannun ƴan bindiga

Duk da yanzu Jaridar Manhaja ba ta da tabbacin faifan, amma ɗan majalisar jihar mai wakiltar Sabon Birni ya tabbatar wanda ke cikin bidiyon mai garin ne.

A cikin bidiyon mai garin na faɗin “ina kira ga ‘yan uwana, abokai cewa yau ne wa’adin da aka sa min ya cika, ina kira da ku taimake ni a yanzu domin ina cikin buƙata.

By ukarofi