
Daga Umar Garba a Katsina
Jami’an rundunar ƴan sanda na musamman sun kama wata mata ƴar shekara 30 mai suna Hauwa Yusuf ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da harsasan bindiga a cikin buhun garri.
An damƙe matar ne a hanyar Abuja-Kaduna lokacin da jami’an rundunar ƴan sanda ke gudanar da buncike akan hanyar.
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar ƴan sandan STS da ke Abuja.
Adejobi ya ƙara da cewa, Yusuf ta amsa cewa wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya yi ƙaurin suna a jihar Katsina, Aminu Basulluɓe ne ya aika matar don ta kai wa wata dabar ɓarayin daji makaman a sansanin Danum Madam dake jihar Katsina.
Adejobi ya ce, “A ranar 14 ga watan Agusta, 2024, jami’an STS sun kama wata Hauwa Yusuf mai shekaru 30 wadda ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina.
“An kama wadda ake zargin ne a hanyar Lafia, jihar Nasarawa zata nufi jihar Katsina, a cikin wata mota ƙirar Sienna da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. A yayin gudanar da bincike, an same ta ɓoye da bindiga ƙirar AK-47 guda da kuma ƙunshin alburushin bindigar AK 47 guda huɗu da aka ɓoye a cikin farin buhun gari.”
Da take amsa tambayoyin manema labarai, Hauwa’u Yusuf ta ce ba ta san an ɓoye bindiga a cikin buhun ba.
“Ban san cewa makamai ba ne a ciki. Ce mani suka yi gero ne, ni ma ko da na ga buhun abun ya bani tsoro” Inji ta.
