LAFIYA UWAR JIKI: Olsa (gyambon ciki)

Spread the love

Gabatarwa 

Wannan ciwo na olsa, wato gyambon ciki, ciwo ne da yake ci wa al’umma da yawa tuwo a ƙwarya. Haƙiƙa mutane da yawa na fama da olsa. Babu ranar da za ka je asibiti ɓangaren “gastro” ba ka samu wanda ya zo da ƙorafin olsa ba. 

Mutan gari (laymen) a gurinsu in an ce olsa, to ciki ta ke kamawa. Amma a matsayina na  malamin lafiya, na san akwai olsa iri daban daban da ke kama sassa na jikin ɗan adam. Ba zan kaiku nan ba, zan tsaya a iya olsar da ke kama kayan ciki kaɗai. 

Da ina tunanin zan iya gama rubutu akan olsa a zama ɗaya, wato sai da na zauna na fuskanci cewa abin babba ne. Matukar so na ke a fahimta kuma a gane, to sai da na dinga yin rubutun da kaɗan kaɗan har na gama. 

Yau in sha Allah zan yi bayani akan me ce olsa ko gyambon ciki, inda ta ke kamawa, nau’o’inta, da kuma yadda ta yaɗu a duniyarmu. 

Me ce ce olsa?

Olsa Kalmar likitanci ce da ke nufin tawaya ko katsewa a shimfiɗar wane sashe na jiki. Misali idan kika/ka kalli fatar da ke tsakanin wuyan hannunka zuwa gwiwar hannu, shimfiɗar fata ce a wajen ko? To idan wani rauni ya samu ko wani ciwo ya fito a kan fatar, za mu iya kiran wannan da olsa. 

Olsar da za mu mayar da hankali anan it ace wadda ke fitowa akan ‘titin abinci’ wato Peptic Ulcer Disease. Abida da nake nufi da titin da abinci ke bi shi ne hanyar wucewar abinci tun daga baki har izuwa dubura. Sai dai gyambon ciki akwai gurare 3 da yafi kamawa a wannan titin. 

Bigiren olsa 

1. ƙarshen bututun abinci (wato ƙarshen ƙasan jannai)

2. tumbi (jakar da ke tare abinci tare da narka shi)

3. farkon sashen ‘yan hanji ko ƙaramin hanji

Ire-iren Olsa

Saboda waɗannan gurare da olsa ke kamawa, an kasa ta izuwa:

1. Olsar ƙaramin hanji (kaso sittin zuwa saba’in na olsa)

2. Olsar Tumbi (kimanin kaso talatin)

3. Olsar jannai (ba ta da yawa, kaso 1 zuwa biyu)

Yaɗuwar Olsa

Akwai olsa a ko ina a faɗin duniya. Ma’ana ta na kama baƙi kuma ta na kama fari. Amma akwai banbanci. 

Su masu jajayen kunnuwa da kuma ƙasashen da su ka ci gaba, a cikin al’ummarsu, kaso 10 bisa ɗari ne su ka taɓa samun ciwon olsa. Anan kuwa kasaashe masu tasowa, kaso 30 ne. 

Olsa ta na kama maza kuma ta na kama mata. Amma tafi kama maza. Sai ka ga maza 2 masu olsa sannan za ka ga mace 1. 

Maza sun fi yin olsar da ke kama hanji, kuma dama a jumulla, olsa ta fi kama hanji fiye da tumbi kamar yadda na faɗa a baya. Su kuma mata sun fi yin olsar da ke kama tumbi. Bincike ne ya nuna hakan. 

Sannan kuma olsa ta fi kama manya fiye da yara. 

Olsar tumbi tafi yawa a manya da dattijai

Olsar hanji ta fi yawa a matasa da masu ƙananan shekaru (20-40)

Ku ci gaba da bibiya ta domin kawo ƙarashen wannan rubutun. In sha Allah zan kawo yadda olsa ke kama mutum, alamominta, da illolinta, da wahalhalun da ta ke jefa mutum da kuma dabarun kiyaye tashinta.

Ku tara a mako na gaba da yardar Allah.

Naku, Abdullahi Mustapha Ibrahim Abdullahi

By ukarofi