Sojoji sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta zaman lafiya a Kudancin Kaduna

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Zonkwa Selected da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta zaman lafiya da rundunar kiyaye zaman lafiya ‘Operation Safe Haven’ ta shirya a Kudancin Kaduna.

Ƙungiyar dai ta lashe gasar ce bayan ta lallasa takwararta ta Golden Balley da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a da ci 3-1 a wasan ƙarshe da aka buga a sabon filin wasa na garin Kafanchan a da ke Jihar Kaduna.

Da ya ke jawabi bayan kammala gasar, Kwamandan Rundunar ta OPSH mai hedkwata a Jos, babban birnin Jihar Filato, Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali, ya ce sun shirya ta ne domin bai wa matasa damar nuna bajintarsu tare da ƙara musu danƙon zumunci baya ga tallafa musu da kuɗi don samun abin yi.

Janar Ali, ya ce, harkar wasanni na ɗaya daga cikin abubuwan da aka yi amanna suna ƙara danƙon zumunci tsakanin matasa, inda ya ce, hakan ne ya sa suka shirya gasar don ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daga ƙananan hukumomi biyar da ake yawan samun tashin hankali a Kudancin Kaduna.

“Mun yi imani cewa zaman lafiya mai ɗorewa za a same shi ne kawai idan an shigo da duk wani mai ruwa da tsaki cikin lamarin musamman matasa tare da sama musu abin dogaro.

“Hakan ne ya sa muka janyo matasa tare da shirya musu wannan gasar baya ga sauran abubuwa da muke yi na farfaɗo da zaman lafiya,” inji shi.

Ya kuma yaba wa rundunarsa da ke barikin soji na Kafanchan ƙarƙashin jagorancin Kanar Timothy Opurum da suka samar da zaman lafiyar da ya ba da damar buga wasan ba tare da tashin hankali ba.

Rundunar, tare da hadin gwiwa da cibiyar Beautiful Gate Handicap da ke garin Jos sun raba kekunan guragu guda 30 ga guragun da aka zaƙulo daga Ƙananan Hukumomin biyar.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kagoro Utd da ke Ƙaramar Hukumar Ƙaura ce ta zo ta huɗu inda aka basu takardar cek na Naira 200,000, sai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gwantu United daga Ƙaramar Hukumar Sanga ta zo ta uku inda aka basu kyautar N300,000 yayin da Golden Balley da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a ta zo ta biyu tare sa samun kyautar N500,000 sai zakarun gasar, Zonkwa Selected da aka ba kyautar N700,000.

Ƙungiyar da tafi kowacce ita ce Jama’a Emirate FC sai Bogoro Alƙali daga ƙaramar hukumar Kauru ya samu kyautar wanda yafi zura ƙwallaye (bayan ya zura ƙwallaye 5), yayin da Kumai daga ƙaramar hukumar Ƙaura aka ba shi kyautar ɗan wasa mafi ladabi.

Baba Audu daga ƙaramar hukumar Jama’a ne aka ba kyautar ɗan wasa mafi bajinta (Best Player).

Daga cikin manyan bakin da suka halarci gasar akwai Kwamishinan Raya Yankin Kafanchan; Misis Phoebe Sukai Yayi da Kwamishinan Wasanni na Jihar Kaduna shugabannin ƙananan hukumomin Jama’a da Sanga da Kauru da Sarkin Jama’a; Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu da wakilan Sarakunan Zikpak da Chawai da Attakar da Kaninkon da shugabanin jami’an tsaro na ’yan Sanda da na Sibil Difens da na Hukumar Kiyaye Haɗurra da ’yan aikin sa kai na KADVS da sauransu.