Samar da tsaro babu wutar lantarki a Nijeriya almara ce – Alhaji Ashiru Gezawa

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

An bayyana cewa duk wani shugaba da zai zo nan gaba a Nijeriya koma na yanzu da ya ce zai inganta tsaro da tattalin arziƙi da duk wani cigaba ba tare da ya samar da wadataccen hasken wutar lantarki ba a Nijeriya to abu ne da ba zai yiwu ba kuma almara ce ko kuma yaudara.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Ashiru Ali Muhammad Yammusa Gezawa, Shatiman Sardaunan Alagwado a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis ɗin makon jiya.

Har wa yau, Yammusa Gezawa ya ƙara da cewa babbar matsalar mu a yau ita ce rashin aiki ga miliyoyin matasa wanda kuma ke haddasa rashin tsaro sakamakon tsananin talauci da tsadar rayuwa wanda kuma ba abinda zai yi maganin wannan cikin sauri sai samar da aiki ga miliyoyin matasan ƙasar nan, wanda kuma hakan ba za ta samu ba sai kamfanonin Nijeriya na aiki ka’in da na’in.

Gezawa ya ƙara da cewa aikin kamfanoni ba zai yiwu ba sai an samar da hasken wutar lantarki a Nijeriya, wanda a cewarsa yin hakan shine zai sa a samu bunƙasar tattalin arziƙi da farfaɗo da darajar naira.

Saboda haka, Gezawa ya yi kira ga shugabanni kan su tashi tsaye wajen kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi al’ummar Nijeriya musamman rashin tsaro, rashin wadataccen ruwan sha, kiwon lafiya da kuma daƙile tashin gwauron zabi na farashin kayayyakin masarufi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *