Ranar Dimokuraɗiyya: Kada ku maida lamarin zaɓen 2023 na ‘a-yi-rai-ko-a-mutu’, Buhari ga ‘yan siyasa

*Ya ba da tabbacin gudanar da sahihin zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman kuma ‘yan siyasa da cewa, a lura a kuma kiyaye kada a maida sha’anin zaɓen 2023 ya koma na a-yi-rai-ko-a-mutu.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa ranar Lahadi kan bikin ranar Dimokuraɗiyya ta 2022.

Yayin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe a 2023, inda talakawan ƙasa su zaɓi wanda suke ganin ya fi cancanta ya zama magajinsa.

Don haka, ya hori ‘yan siyasa da magoya bayansu kan su gudanar da yaƙin neman zaɓensu a tsanake.

A cewar Shugaban, “Yayin da muke shiga lokacin yaƙin neman zaɓe na babban zaɓe mai zuwa, ya zama wajibi mu nuna halin kamala wajen gudanar da harkokin neman zaɓe da kuma kaɗa ƙuri’a. Kada mu ɗauki lamarin tamkar na a-yi-rai-ko-a-mutu.

“Dole mu tuna cewa ita dimokuraɗiyya aba ce da ta danganci ra’ayin masu rinjaye, wanda dole ne a samu waɗanda suka yi nasara, haka ma waɗanda suka sha kaye.

“Don haka nake amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan takara da su gudanar da harkokinsu cikin lumana da mutunta abokan hamayya.

“A matsayin shugabanni, dole ku nuna kyawawan ɗabi’u, sannan ku sani cewa duniya tana kallonmu, haka ma Afirka ta sanya wa Nijeriya ido don koyi da salon shugabancinta mai nagarta…,” inji shi.

Shugaba Buhari ya ce, a tsakanin shekaru bakwai da suka gabata gwamnatinsa ta bakin ƙoƙarinta wajen inganta lamarin zaɓe ta hanyar samar da dokokin da suka dace din bai wa ‘yan ƙa zarafin kaɗa ƙuripa ciki sauƙi da lumana gami da kare musu ƙuri’unsu.

Ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara, ita ce ranar da Nijeriya ta ware don bikin Ranar Dimokuraɗiyya.

Jawabin Buharin, shi ne jawabinsa na ƙarshe kan Ranar Dimokraɗiyya da ya yi wa ‘yan ƙasa kasancewar wa’adin mulkinsa zai cika kafin zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta baɗi.