Daga BASHIR ISAH
‘Yan bindiga sun sako fasinjojin da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a lokutan baya.
Hakan ya biyo bayan sasantawar da aka yi ne tsakanin Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindigar.
Ɗan jarida na kusa Sheikh Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu ya bayyana cewa, mutum 11 da lamarin ya shafa ne ‘yan bindigar suka sako su a ranar Asabar.
Ya ce, an kwashi waɗanda aka sakon baki ɗayansu zuwa Abuja don duba lafiyarsu a bisa umarnin Shugan Ƙasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a haɗa su da ‘yan uwansu.
Mamu ya ƙara da cewa, wasu tsoffin manyan sojoji da kuma wani fitaccen Farfesa na daga cikin waɗanda suka taimaka wajen sako fasinjojin.
