Ta tabbata Gwamnan Zamfara na yunƙurin sauya sheƙa zuwa APC, inji majiyar jam’iyyar

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wata majiya mai ƙarfi daga jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, ta tabbatar da yunƙurin canza shekar Gwamna Dauda Lawal daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC nan ba da jimawa ba.

Wani jigo a APC a Jihar da ya buƙaci Wakilin Jaridar Blueprint ya sakaye sunan sa, ya bayyana hakan a hirar da yayi da Wakilin mu ta Wayar tarho yau Asabar.

A cewarsa, Gwamnan ya gabatar da kudurinsa na dawowa Jam’iyyar APC Mai mulki a Nigeria daga Jam’iyyar SA ta PDP kwanaki hudu da suka gabata Kafin wucewarsa Kasa Mai Tsarki don yin Umra.

A cewar majiyar, acikin sharuɗɗan da Jam’iyyar APC zata gindayawa Gwamnan harda daukar kaso 60 na Jam’iyyar su bashi Kashi arba’in 40.

“Inaso in sanar da Duniya cewar tabbas Gwamnan Jihar mu ta Zamfara ya tuntubi Jam’iyyar APC a Jihar a hukumance cewar yanason ficewa daga jam’iyyar sa ta PDP zuwa APC.”

Majiyar ta kuma ce akwai sharuɗɗan da Jam’iyyar APC take da su kafin ta amince da gwamna Dauda Lawal ya shigo cikinta daga PDP gabanin zaɓen 2027.

By Babaji