
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yanayi na ƙoƙarin kafa tarihi, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami ta kai ziyara a Fadar Shugaban Amurka, wato White House domin murnar lashe gasar MLS Cup da ta yi a 2025.
Saidai armashin ziyarar ya ragu a sakamakon rashin ganin ɗaya daga cikin tawagar ƙungiyar kuma sanannen tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa.
Yayin da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi ta je Birnin Washington D.C., inda Shugaba Donald Trump ya karrama ta, David Beckham bai samu halarta ba saboda wani muhimmin al’amari da ya je yi a Nahiyar Yurop.
Wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan ƙungiyar Barcelona kamar su Sergio Busquets, Jodi Alba da Luis Suarez na cikin tawagar da suka je bikin al’adar na zakarun wasannin Amurka a White House.
Da fari, an shirya cewa Beckham zai je ziyarar tare da sauran ‘yan ƙungiyar, inda daga bisani ya cigaba da zama a Yurop domin nuna goyon baya ga iyalinsa da ke gudanar da babban taro na kwalliya.
A cewar wani rahoto da CN ya ruwaito kuma White House ta tabbatar, tsohon ɗan wasan na Manchester United ya fifita hidimar iyalinsa sama da bikin karrama ƙungiyar.
