
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane 16 ciki har da matar wani kwamandan ‘yan bijilante da ƙanwarta da kuma ‘ya’yan fasto guda huɗu ne aka yi garkuwa da su bayan wani hari da ‘yan bindiga suka ƙaddamar a ƙauyen Peze da ke yankin Byazhi a Kubwa na Ƙaramar Hukumar Bwarin Birnin Tarayya Abuja.
An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun je yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai tsakanin ƙarfe 9:30 da 10 na daren Talata, inda suka riƙa shiga gidajen jama’ar garin.
Wani mazaunin yankin da ya gana da ShaharaReporters ya ce maharan sai da suka taru a wani kango da ke fuskantar gidansa kana daga bisani suka ƙaddamar da harin nasu.
A cewarsa, sun yi barazanar halaka dukkan wanda ya ƙi buɗe ƙofa ta hanyar halaka kowa a gidan da irin haka ya shafa.
Ya bayyana cewa, ba su samu damar shiga gidan nasa ba, amma sun yi nasarar garkuwa da mutane da dama a wasu gidaje.
Daga cikin waɗanda aka sace akwai ‘ya’ya huɗu na wani fasto a yankin. Al’amarin ya faru ne a lokacin da faston ba ya gida.
Haka kuma harin ya shafi iyalin wani kwamandan ‘yan bijilante da ke taimaka wa ƙauyen wajen bayar da kariya akan ayyukan ‘yan bindiga. Sun kuma yi awon-gaba da ƙanwar matar, wadda ta kai musu ziyara kwana uku gabanin aukuwar al’amarin.
Mazauna yankin suna fuskantar hare-hare daga masu garkuwa da mutanen akai-akai a ‘yan makonnin nan ciki har da wanda ya auku a ranar 4 ga watan Junairu, lamarin da ya tilasta wa jama’ar gari da ‘yan bijilante yin sintiri domin ƙarfafa tsaro.
